Da Dumi Dumi

Sakon Bagizagen Mako

Shugaban Qungiyar Gizago, M. K. Adam Gombe, a dama, yana gaishe da Uban Qungiya, Babban Jojin Jihar Katsina, Mai shari’a Musa Danladi Abubakar
Shugaban Qungiyar Gizago, M. K. Adam Gombe, a dama, yana gaishe da Uban Qungiya, Babban Jojin Jihar Katsina, Mai shari’a Musa Danladi Abubakar

Bakonmu na wannan makon, shi ne Shugaban Kungiyar Gizago na Najeriya, Malam Muhammad Kabir Adam Gombe (08065432898, 08023281167). Ko mene sakon Shugaban na Gizagawa? Ga abin da yake cewa:

Assalamu alaikum Gizagawan Zumunci! Bayan gaisuwa irin ta Musulunci, ina fatar duk kuna lafiya.

Da farko ina kara jaddada godiyata gare ku bisa irin hadin kai da goyon baya da nake samu daga gare ku. Ina fata za ku ci gaba da ba mu goyon baya da hadin kai.

Ina kuma kara kira ga shugabannin jihohi su kara zage dantse wajen kiran kananan tarurruka da suka saba gabatarwa, tare da kai ziyarce-ziyarce gidajen marayu da na kangararru da kuma taimaka wa juna a duk lokacin da wani al’amari ya taso.

Daga karshe ina kara mika godiyata ga tsoffin shugabanni a matakin ƙasa da jihohi, kan gudunmawar da suke bayarwa ta fuskar kudi da shawarwari. Ina matukar jin dadi da godiya kwarai da gaske. Allah Ya saka da alheri, Ya kuma kara mana zumunci.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya