✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakon Bagizagen Mako

Bakonmu na wannan makon, shi ne Shugaban Kungiyar Gizago na Najeriya, Malam Muhammad Kabir Adam Gombe (08065432898, 08023281167). Ko mene sakon Shugaban na Gizagawa? Ga…

Bakonmu na wannan makon, shi ne Shugaban Kungiyar Gizago na Najeriya, Malam Muhammad Kabir Adam Gombe (08065432898, 08023281167). Ko mene sakon Shugaban na Gizagawa? Ga abin da yake cewa:

Assalamu alaikum Gizagawan Zumunci! Bayan gaisuwa irin ta Musulunci, ina fatar duk kuna lafiya.

Da farko ina kara jaddada godiyata gare ku bisa irin hadin kai da goyon baya da nake samu daga gare ku. Ina fata za ku ci gaba da ba mu goyon baya da hadin kai.

Ina kuma kara kira ga shugabannin jihohi su kara zage dantse wajen kiran kananan tarurruka da suka saba gabatarwa, tare da kai ziyarce-ziyarce gidajen marayu da na kangararru da kuma taimaka wa juna a duk lokacin da wani al’amari ya taso.

Daga karshe ina kara mika godiyata ga tsoffin shugabanni a matakin ƙasa da jihohi, kan gudunmawar da suke bayarwa ta fuskar kudi da shawarwari. Ina matukar jin dadi da godiya kwarai da gaske. Allah Ya saka da alheri, Ya kuma kara mana zumunci.