✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakon Gwamnan Bauchi daga inda yake killace

Masu iya magana kan ce “Motsi ya fi labewa”. Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya fitar da wani sako daga inda yake killace yana jinya.…

Masu iya magana kan ce “Motsi ya fi labewa”. Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya fitar da wani sako daga inda yake killace yana jinya.

Gwamnan ya aike da sakon ne ga masu yi masa fatan samun lafiya tun lokacin da sakamakon gwaji ya tabbatar yana dauke da cutar coronavirus wadda yanzu ta zama annoba a fadin duniya.

Ga abin da gwamnan ke cewa:

“Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki Mai kowa Mai komai.

“Ina mika godiyata ga Allah da jama’ar Bauchi da Najeriya, musamman shugabanni da malamai.

“Ina son na yi amfani da wannan damar na mika godiyata gare ku, game da  yadda kuka nuna min kauna a halin da na tsinci kaina, duk da na killace kaina saboda wannan cuta da nake dauke da ita ta coronavirus.

“A yanzu haka ba na nuna duk wasu alamomin masu dauke da cutar da suka hada da: tari ko wani zazzabi.

“Zan ci gaba da zama a killace, ina gode wa kwamitin da aka kaddamar don hana yaduwar wannan cutar a jihar.

“Sannan ina godiya ga Shugaban Najeriya da sauran gwamnoni saboda kokarin da suke yi na hana yaduwar wannan cutar.

“Duk da halin da nake ciki a yanzu, ina cikin koshin lafiya. Ina mika sakon godiya ga masu yi min addu’ar samun lafiya, ban taba tsammanin ina da masoya masu kaunata kamar yanzu ba.

“Wannan killacewar ta sa ni na kara fahimtar wasu abubuwan shugabanci, da zarar na fito zan bullo da wasu hanyoyin magance matsaloli.

“Ina rokon Allah Ya kara wa Najeriya karfin tattalin arziki ya kuma magance wannan annobar”.