✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakon mahaifinmu kwana daya kafin rasuwarsa —Ibrahim Balarabe Musa

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna a Jamhuriya ta Biyu ya rasu yana da shekara 84.

A ranar Laraba da ta gabata ce Allah Ya yi wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna a Jamhuriya ta Biyu, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa rasuwa yana da shekara 85.

Babban dan marigayin Dokta Ibrahim Balarabe Musa wanda ya tabbatar wa Aminiya da rasuwar mahaifin nasu, ya bayyana sakon da mahaifinsa ya ba shi kwana daya kafin rasuwarsa.

A cewarsa, duk da rashin lafiyar da mahaifinsu yake fama da shi, ya ba shi umarnin shi da ’yan uwansa su ziyarci gidan marigayi Dan Iyan Zazzau Alhaji Yusuf Ladan wanda ya rasu a ranar Talata, kwana daya kafin rasuwarsa domin yi wa iyalansa ta’aziyya.

Dokta Ibrahim Balarabe Musa ya ce mahaifinsu ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya inda ya ce mahaifinsu ya sanar da su cewa ajinsu daya da marigayi Yusuf Ladan kuma abokinsa ne.

Da yake bayyana marigayin, Dokta Ibrahim ya ce mahaifinsu mutum ne mi son gaskiya kuma ya rasu ne yana mai kaunar talakan Najeriya da kuma kasar baki daya.

Shi ma wani dan marigayin, Alhaji Kallamu Balarabe Musa ya ce babu shakka za su yi kewar mahaifinsu.

A sakon ta’aziyar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana  cewa Najeriya ta yi rashin mutum mai gaskiya, wanda ya kasance gatan mara gata.

A sakon ta’aziyar wanda Garba Shehu ya sanya wa hannu, Shugaba Buhari ya ce marigayi Alhaji Balarabe Musa ya bar wani babban gibi kuma ba za a taba mantawa da shi ba, musamman kan kokarin tabbatar da mulki mai kyau da adalci.

Ya yi addu’ar Allah Ya jikan marigayin Ya ba iyalansa hakurin rashi.

A sakon ta’aziyar, Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya ce ba za a taba mantawa da Balarabe Musa ba, inda ya ce Kaduna na matukar alfahari da tsohon gwamnan.

Gwamna El-Rufai ya yi addu’ar Allah Ya jikansa, Ya yafe kura- kuransa kuma Ya ba iyalansa hakurin rashin.