Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Sakon Sarkin Katsina ga Minista: Fada wa Buhari muna bukatar tsaro

Maimartaba Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman ya fada wa Ministan Noma na Najeriya Audu Ogbe, cewa ya sanarwa shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari manoman Katsina da makiyaya sun kauracewa sana’ar su saboda kaucewa kisan gilla da yin garkuwa da mutane da ake yi a jihar.

Sarkin Katsina ya bayyana hakan ne, lokacin da Ministan Noma da Gwamnan babban bankin Najeriya CBN  Godwin Emefiele suka kai masa ziyara a fadarsa yayin kaddamar da rabon irin auduga ga manoma, wadanda ke shirin fara noman auduga a wannan shekarar 2019.

ADVERTISEMENT