Da Dumi Dumi

Sakon Shugaba Obama ga matasan Najeriya

An kunyatar da ni, an saka ni cikin kaskanci, musamman ganin yadda a karo na biyu da Shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya ziyarci Afrika amma yana tsallake Najeriya ba tare da kafarsa ta taka kasarta ba.
Wasu da aka ce sun san wani abu game da ziyarar, sun bayyana yadda shugabannin Najeriya suka yi ta hakilon ganin cewa Obama ya sanya kasar tamu cikin wadanda zai ziyarta, amma duk da haka ya yanke hukuncin ziyartar wuraren da yake darajawa a Afrika, wato Senegal da Afrika Ta Kudu da kuma Tanzaniya.
Kodayake bai kamata a ga laifinsa ba tashi daya, domin kuwa shekaru hudu da suka gabata, a ziyararsa ta farko a Ghana, ya bayyana baro-baro cewa shi ya fi daraja kasashen da suka tsayu da kafafunsu wajen kare muradun dimokradiyya, wadanda gwamnatocinsu suka fuskanci alkiblar mutunci da kyautata mulki.
Idan zan tuno ma, ga kadan daga cikin abin da Obama ya fada: “Ba wai kawai kasa ta shirya amsasshen zabe ba ne, batun ya wuce nan, domin kuwa abin da ya biyo baya shi ne mai muhimmanci. Cin zarafin al’umma da dankwafar da su suna bayyana ne ta sigogi daban-daban. Bisa ga haka, kasashe da dama sun kasance cikin matsalolin da suka kukume al’ummarsu cikin talauci. Babu kasar da za ta ci gaba, ta samar da arziki, idan shugabanninta suka kasance masu wawushe dukiyarta ko kuma ’yan sandanta suka kasance sayayyu a hannun dillalan muggan kwayoyi. Babu wani dan kasuwar wata duniya da zai ce zai zuba jarinsa a kasar da shugabanninta ke yadda suka so da tattalin arzikinta ko kuma kasar da za ka ga shugaban tashar jirgin ruwa ya kasance dan kashe-mu-raba, barawon dukiyar al’umma. Babu wani mahalukin da zai so ya rayu a kasar da ba a daraja doka da oda, inda ake gallaza wa mutane, ana amsar rashawa da cin hanci. A irin wannan kasar, babu mulkin dimokradiyya, sai dai mu ce mulkin danniya da zalunci. Kuma zan fadi da babbar murya, lokaci ya yi da za a kawo karshen irin wannan tsari na zalunci.”
Ba nan Shugaba Obama ya tsaya da batunsa ba, ya ci gaba da cewa: “Babu kasar da za ta samu ci gaba, inda shugabanta ya banzatar da mutuncinsa, ba ya kulawa da dabi’arsa. Haka kuma babu wani kasuwanci da zai bunkasa a kasar da gwamnati kan karrama muggan barayi da lambobi mafi daraja da girma na kasa, sannan kuma take nada su a manyan mukamai. Babu wani mutum da ya san mutuncin kansa da zai so ya rayu a cikin al’ummar da ake gudanar da al’amura ba tare da gaskiya da adalci da kyautatawa ba, kasar da ma’aikatan gwamnati kan zama barazana ga al’umma, maimakon su kasance masu yi masu hidima.
“Babu kasar da za ta ci gaba, inda kofofin masu rike da madafun iko da na ’yan majalisa suke zama kamar kofofin gidajen kurkuku saboda matakan tsaro, wanda kamata ya yi a ce sun kasance shugabanni masu daraja, masu gaskiya da amana.
“Babu dan kasuwar da zai so ya zuba jarinsa a kasar da shugabanta ke tsoron gaya wa matarsa gaskiya, cewa ba ita ce shugabar kasa ba, ba zai iya gaya mata cewa dukiyar gwamnati ba an samar da ita domin ta yi ta fakaca da wandaka da bukukuwan kece raini da ita yadda take so ba.
“Babu mutumin da zai so ya rayu a kasar da gwamnoni suke tafiyar da dukiyar al’umma yadda ransu ya so, yadda suke macewa da amanar da aka damka masu, su shantake su ki zama ofisoshinsu domin yi wa al’ummarsu aiki. Babu kasar da za ta ci gaba, inda aikin gwamnati kan fara ranar Laraba kuma ya zama aikin raba kwangilar kashe-mu-raba ga abokai, ’yan uwa da iyalai. Sauran ranakun kuwa sai dai a yi ta cin ganima, ana yawace-yawacen babu gaira babu dalili.
“Babu wani mutum da ya san mutuncin kansa da zai so ya rayu a kasar da shugabanninta kan bugi kirji, su kururuta kansu, su ba kansu maki, sannan su rika takama da cewa sun aikata abin kirki.”
Obama ba kawai ya fadi wadannan batutuwa ba ne, a’a, suna ishara ne da yadda ake bukatar canji a Nahiyar Afrika, musamman ma dai a Najeriya. Shekaru hudu ke nan da ya bayyana wannan gaskiya, amma ga shi nan maimakon a samu canji, sai ma kara tabarbarewa da al’amuran suka yi. Al’ummarmu kuwa, a halin da ake ciki, za a iya cewa ba su taba fuskantar tsanani da tabarbarewar al’amura ba kamar na wannan lokacin.
Haka kuma, a 2009, Obama ya yi wa matasa allura, inda ya ce lallai nasarar da za ta samu a nan gaba, matasa ne za su samo ta. Kamar yadda ya ce: “Kuna da karfi da tasirin da za ku titse shugabanninku, ku gina ingantattar kasa wacce za ta zama abin alfaharin al’umma.” Ya karfafa wa matasan Afrika gwiwa cewa lallai idan suka jajirce, suka yi aiki tukuru, za su samu nasarar kawo canji. “Wannan ba mai sauki ba ne, sai kun jajirce kuma ba yanzu-yanzu nasarar za ta zo ba, sai nan gaba.” 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya