Sakonni: Barka da Ramadana

Dalibai mata na daukar darasiAssalamu Alaikum
A batu mara waskiya, dole mu mika dimbin godiyar mu ga Mai-duka wanda ya kawo mu wannan wata mai tarin albarka, ya kuma nuna mana karshen wannan rikita-rikita wadda ta bai wa Manjo janar Babban Dogari Shugaba AabaCa, damar wartsakewa da yawatawa da mike kafa gami da shan iskar duniya.
Dama dai ladabin da Masana kuma Masu gadon Manzanni ke nusar wa a cikin wannan watan bai wuce na kusantuwa da Allah Ta’ala ba, a bar zambo, da keta gami da algush. Masu sabo su saduda salun-alin izuwa tafarkin gaskiya. Wanda kuma aka yi wa laifi sai ya mance, ya yafe, gami da mika kaddarar aukuwar abin ga Sarkin Sarakuna.
Don haka nake ganin ‘yan makaranta ya kamata mu ladabtu da wadannan halaye, ba iya mu ba, har da sauran makaranta. Mu bar  ziyartar makarkata sai dai makabarta da makaranta. Mu bar yawon zaman-ci, sai dai yawon sadar da zumunci, haka kuma kada mu dukufa addu’ar neman Na-goro, sai dai addu’ar neman gafara daga Allah Ta’ala.
A karshe ina taya daukacin Musulmi barka da Ramadana, ina kuma addu’ar neman zaman lafiya a kasar mu, batun Hamza kuwa, fata nake Allah yasa kada wannan hukunci ya zamo Ta-leko-ta-koma.
Daga Sadik Tukur Gwarzo 08060869978.

Arewatawa a kwankwadi mai kararrawa
Sallama, rashin nadama duk su tabbata ga ilahirin ma’abota da makaranta na wannan shafin bai daya. Babu waskiya, Arewatawa sun koka, tura takai bango, ta ko ina kururuwa muke yi don neman agaji.
 A Arewa ne fa Gwamnan Jangwam, wanda a kullum yake hakilon jona Arewatawa da mulkin gudun loko. A nan ne Tsoho Babu-Manga sai Damanga a Jihar da Fullo ke Damawa da Labaran mai Mammako da wasunsu, masu akidar ‘yan lingabu suke wadanda babu kalmar Tallafa wa Talaka a kamus din rayuwar su. Dama kuma babbar matsalar da ta dabaibaye yankin namu na Arewa bai wuce na rashin kishin al’umma ba, daga wasu masu fada aji a yankin wadanda suka fi damuwa da cika aljihunansu maimakon fitar da al’umma daga kangi.
  Kowa dai na ganin yadda salon mulkin kasar nan yake, wato ‘yan mowa da ‘ya’yan bora wanda hakan ke haifar da rashin zama lafiya a kasa baki daya, don haka muna rokon Allah ya kawo mana sauki koda ta hanyar jam’iyar ‘yar fi-siy ce, wadda muke sa-ran za ta yi maganin aji-garau, wato jam’iyya mai sunan magani mai kararrawa. A huta lafiya.
Daga Sadik Tukur Gwarzo 08060869978

Sako ga Dodo
Sallama marar iyaka ga direban alli babban dodo uban dodonni,da fatan kana cikin koshin uwar jiki? idan haka ne toh madallah da tafi dalla-dallah wai ni kam Dodo ya aka yi muka ga kwana biyu makaranta shiru da fatan dai lafiya?
Daga Ashaka dan mutan Katsinawa.

dauki muke nema
Sallam ga masu bautar sarki sili, kai jama’a ku  gane mini hanya  wai makaho yaso gulma.yanzu haka masu koyon watsatstsake da bude waggen litattafai na makarantar  fallen takalmin Gwamnatin Tarairaya ta garin Ka-zauna-a-zaure da ke Jihar Jijjiga-ciyawa, sun shafe makonni manuniyar kasa suna zaman dabara a matsugunnan iyayensu, su kuwa direbobin allin wannan makaranta suna ta hutun hota ro-ro, don ba sa zuwa ko roro ballan tana su kalato ko da dan wani abu, wai da sunan zagwalin kwadago. Bayan sun gama tatuke lalitar ‘ya’yan talakawa wajen biyan kudin zangon darasi na sababbin dalibai ba tare da ragin ko asi ba. To Buwayi ya  gyara mana.
Daga: dalibin Jihar Tumbin giwa Buhari Musa dambatta 07062885413.

ADVERTISEMENT

Tallace-tallace  ko lallacewa?
Bayan gaisuwa irinta masu fuskantar alkibla don gaida Mai-duka sili, ina jinjina ga ‘yan uwana daliban wannan makaranta ta Dodorido dama uban tafiya Farfesa DODO. A wannan lokaci idan muka dauki yadda yawan tallace-tallace ya zama ruwan dare a duk inda ka zagaya za ka ga yara kanana suna tallace-tallace akan tituna zuwa kamfanoni da masana’antu, har da sauran wurare da ake hada-hadar yau da kullum don haduwa da masu sayen abin da suke talla. A wani ban gare kuma sai na nace lala cewa ce kawai  ba don komai ba, don za kaga abin da suke tallar bai taka kara ya karya ba ta haka ne idan an sami rashin sa’a sai a sa yaran a sayi Mai-duka ya kiyaye mu da aikin da na sani . Talla ta kasu kashi kashi a wannan lokaci, akwai masu talla na zama waje daya, akawai masu talla na zagaya wa waje waje, akwai masu talla na kan titi kawai, kamar danja ko bakin titi, mata da maza yara da manya.
Daga dalibar Jihar Tumbin giwa, Saudat Ali Ilu (UMAN HAIDAR) 08138296838.

Share