✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakonnin Fadar FDk

  Kamar yadda muka saba, yau ma ga mu a wannan sashi na sakonnin Fadar FDk. Ina kara kira ga masu turo sako da su…

 

Kamar yadda muka saba, yau ma ga mu a wannan sashi na sakonnin Fadar FDk. Ina kara kira ga masu turo sako da su rika rubuta cikakken suna da adireshi tare da lambar waya, idan kuma mutum ba ya son a buga lambarsa, sai ya bayyana a kasan sakonsa. Ga lambar da za a turo sako: 08098157899 ko I-mel: [email protected] A wannan makon, ga sakonnin da suka samu shiga:

Ina godiya

FDk, ina so ka ba ni dama in yi godiya ga dukkan masoyan wannan dandali da suka kira ni, wasu sun aiko mani da sakon fatan alheri na samun aure a wannan fili na Dausayin kauna. Allah Ya saka maku da alheri, Ya bar zumunci, amin. FDk, don Allah ka sanya mana albarka.

Daga Umar Kano, Sarkin Yakin FDk (07035438533)

Madalla da wannan labari kuma ina yi maku, kai da amaraya fatan alheri. Allah Ya kadarta a yi aurenku lafiya kuma Ya albarkace ku da zuri’a ta gari da yalwar arziki. – FDk.

Mata ku daina yaudara

FDk, ya aiki? Allah Ya kara wa jaridar Aminiya farin jini. Don Allah ka fada wa mata cewa su yi hakuri su daina yaudarar maza haka nan.

Daga Sani Sidi (07036275613)

Fatan alheri

Fatan alheri gare ka FDk, da fatan kana cikin koshin lafiya. Ina so ka ba ni dama domin in mika gaisuwata ga babban yayana, wato Sarkin Yakin FDk. Allah Ya daukaka darajarsa don son Nabiyyi Rahamati, amin.

Daga kanwar Sarkin Yaki

Jinjina ga masoyiyata

FDk, barka da aiki da fatan ka dawo daga hutu lafiya. FDk, yau jinjina zan yi ga masoyiyata, sarauniyar ’yan matan duniya, sahibata, farin cikin raina, abokiyar rayuwata duniya da lahira, uwar ’ya’yanmu; wadda tun da Allah Ya sa na fara soyayya, babu wata ’ya da na sa ta a cikin ruhina, na ba ta kaina gaba daya kamar wannan baiwar Allah saboda diyar manyan mutane ce. FDk, wallahi tana da tarbiyya, ga sanin ya kamata, ga ilimi a kowank fanni. Tun kafin mu ga juna muka yi wa kawunanmu alkawarin in sha Allahu za mu zauna a tare a matsayin mata da miji. Wannan ba wata ba ce, Hauwa ce ’yar Gombe.

Daga Mamman S. dancharanchi, Deidei Abuja (09038788770)

Murnar aure

FDk, jarumi kuma gwaninmu, gaisuwa a gare ka. Duba jaridar da na yi ta wannan Juma’ar, na ga abin farin ciki; ma sha Allah! Fatan alheri ga FDk tare da Umar Kano Sarkin Yaki da samun matar aure a filinmu na Dausayin kauna. Allah Ya tabbatar da alherinsa cikin wannan al’amari, Ya kuma kai mu ranar biki, Ya sa a yi lafiya, Amin Ya Karim.

Daga Khadijat Tahir (Majidadin FDk)

Na samu budurwa

Fatan alheri ga duk ’yan uwa da abokan arziki. Alhamdu lillah, Allah Ya ba ni budurwa wadda nake kaunarta, ita ma tana kaunata. Gaskiya yanzu ina cikin farin ciki da walwala, na gode.

Daga Hon. Abdullahi Ma’aruf G/dutse

FDk, ina so ka mika mani dinbin gaisuwata ga masoyiya Maryam Birnin Kebbi, wadda na samu wannan fili naka mai albarka na Dausayin kauna. Allah Ya bar zumunci.

Daga Nafi’u A. B. Sakkwato

Gaisuwa

FDk, ka bar mu da kewa kwana biyu. Don Allah Malam a mika mini Barka Da Sallah ga masoya Annabi (SAW).

Daga Muhammad Yahaya Sakkwato (08066099413)

Mu daina yaudara

Fatan alheri a gare ka FDk. Don Allah ka ba ni dama in yi kira ko tsokaci ga ’yan uwana ma’abota wannan dandali, da mu kasance masu fada wa juna gaskiya da rike amanar juna; domin wasu samari da ’yan matan sukan yi amfani da wannan dandali wajen yaudarar juna. Mu sani, duk abin da ba ka so a yi maka, kada ka yi wa wani. Samari mu daina karya, ’yan mata a daina yaudara, domin ku ne kan gaba wajen iya yaudara.

Daga Murtala Ahmed Abubakar (07068295953)

Na ji dadi

Alhamdu lillahi! A gaskiya na ji dadin dawowar Dausayin kauna. Ina fatan ka yi Sallah lafiya.

DagaAbubakar Sakkwato (08133981593)