✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakonnin Fadar FDK

Darasin Labarin Farida Wannan labarin na nuni da jan hankali ne ga mata masu bakin kishi da cewa daga karshe fa zai zama nadama. To…

Darasin Labarin Farida

Wannan labarin na nuni da jan hankali ne ga mata masu bakin kishi da cewa daga karshe fa zai zama nadama. To kuma duk ba a nan gizo ke sakar ba, idan an bi ta barawo sai a bi ta mabi sawu. Wani lokacin, wasu mazajen ne ba su shuka adalci a zamantakewar aurensu, tsakaninsu da matansu na gida, wadanda suka riga suka aura. Shi ya sa wasu matan za su ga cewa idan fa ya kara auren nan, to ba zai yi adalci a tsakaninsu ba, sai ta shiga rudani daga lokacin da ta fahimci hakan. Illa iyaka maza don Allah mu kara jin tsoron Allah tsakaninmu da matanmu na sunna.

Daga Muhammad Hassan Danbaza, Zamfara Radio Gusau, 07068040761

Mu daina cutar da mata

FDk, fatan alheri a gare ka da dukkan ma’abota wannan fili. Bayan haka, ina kira ga ’yan uwana maza, don girman Allah mu gyara halayyarmu wajen yaudarar kannenmu mata, wallahi ana cutar da su. Da fatan ’yan uwana maza za mu gyara.

Daga Aminu Bature Marmara, 08133310399

Shawara nake nema ku ba ni. Akalla zan kai shekara ashirin a duniya amma duk tsawon lokacin da na yi, ban taba zuwa makaranta ba sakamakon na tashi ba ni da gata amma yanzu na samu saurayi da ya ce zai dauki nauyin karatuna. Amma yanzu na iya karatun Hausa, zan iya karanta jarida amma ban iya karatun Turanci ba kuma ba na jin Turanci sosai. Ku ba ni shawara, shin lokaci bai kure mani ba?

Daga Hauwa’u Haidar Suleja, 08145473288

Shawara: 

Malama Hauwa’u, maganar neman ilimi gaskiya ba ki makara ba, amma da son samu ne, in dai wannan saurayi da gaske yake yana kaunarki, kuma zai dauki nauyin karatun naki, to kamata ya yi ya aure ki; alabashi kina gidansa sai ya kyale ki ki ci gaba da karatunki hankali kwance. Allah ba da sa’a. – FDk.

Mu hada zumunci babba

FDk ina gaida dukkan masoya wannan fili baki daya. Ina kuma rokon Allah Ya sa wata rana dukkan masoya wannan fili mu hadu gaba daya don mu ga juna, mu sada zumunci tsakaninmu, kila har ma so da kauna ya kullu a tsakanin wasu, har auren so da kauna ya kullu. Sannan ogan wannan fili na FDk ya dausayar da mu Dausayin kauna. Allah shi kawo wannan rana. Masoya ku ce amin. 

Daga Hussain danjari Umar Kadarko Katsina, 08038810162

Shawara ga masoya

A duk lokacin da ka ga yarinyar da kake so tana yi maka wadansu dabi’u ko nuna maka wasu halayen da kake ganin ba su kamata ba, a matsayinta na masoyiyarka; to ka bincika. Watakila ba kai mata ba ne ko ba ka da wasu halaye da take so ko watakila ba ka da wasu siffofin da take so. Haka abin yake a bangaren mazan ma, amma ya kamata a daina boye wa juna. Idan kuka ga masoyanku ba su yi maku ba, ku dinga fada wa junanku gaskiya. Hakan ma na da kyau. A rage yaudara da nuna ana son mutum alhali a zuciya da ruhi da gangar jiki ba haka ba ne. Dafatan Allah Ya hada kowa da masoyin gaskiya. Fatan alheri gar eku ma’abuta filin Dausayin kauna.

Daga Salisu Young Dr. Abuja, 08107022503

Gaisuwa ga FDk

Assalamu alaikum, ina mika gaisuwa ga babban yaya FDk da kuma masoyan wannan fili. Ina sa ran kowa na lafiya. Samari, shawara a gare ku, ku zama masu rikon amana. Sauran bayani yana ga kanwata, Ummi Mairiga.

Daga Aminatu Abubakar

Ka zama Shugaban Soyayya

FDk ka zama HOD (Shugaban) Soyayya. Allah Ya kara basira.

Daga Isah Mato Bichi, 08062212290

Zan shiga fadar FDk

Gaisuwa ga FDk, da fatan kana nan lafiya. Kamar yadda Ameena Lawal ta ce ita bakuwa ce a wannan filin, ni ma ko zan samu shiga fadarka?

Daga Sulaiman Idris Bauchi, 09035865776

Na samu masoyiya

Assalamu alaikum Shugaban Masoya na Afirka gaba daya. Ya aiki, ya hakuri? Ina so in ba ka labarin cewa na samu wata budurwa mai sona, kyakkyawa, son kowa kin wanda ya rasa. Na gode da wannan shafi mai albarka.

Daga Shamsu Kano Gezawa, 07066796978

Na kasa barin sonta

Salamu alaikum FDk, Allah Ya kara maka daukaka. Wallahi na samu kiraye-kirayen waya daga wajen mutane da yawa a kan cewa yarinyar nan in cire ta daga zuciyata. Wallahi na yi kokarin cire ta amma na kasa.

Daga Anas, 08031171409

Amsa:

To, Malam Anas, tun da ka kasa cire ta daga zuciyarka, sai ka ci gaba da juriyar hakurin duk abin da ya zo maka ta hanyar kaunarta. Allah Ya kiyaye matsala, amin. – FDk.

Fatan alheri

Assalamu alaikum, FDk, ya aiki Allah Ya kara basira.

Daga Abdurrahman Gayawal-Kano, 09027777329

Mu daina yaudara a FDk

Fatan alheri a gare ka FDk. Don Allah ka taimake ni ka ba ni dama na yi kira ga ’yan uwana ma’abota wannan dandali mai albarka, bisa sanya lambar wayarsu a wannan dandali. Hakan ba laifi ba ne amma yana da kyau samari ko ’yan mata mu daina kiran junanmu domin yaudara. Shafin FDk shafi ne mai farin jini. 

Daga Murtala Ahmed Abubakar Kwalli, 07068295953

Fatan alheri

FDk, ina yi maka fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya kara maka lafiya da juriya, Ya kuma ba ka sa’a a kan duk abin da ka sa a gaba na alheri.

Manniru Kurna-Kano, 07035204863

Tambaya ga mata

Fatan alheri, ni tambayata ita ce, me ya sa mata ba su son auren mai mata?

Alhaji Kabiru Jajira-Kano, 09097486318

Maza ku ji tsoron amana

FDk, da fatan kana lafiya, ya kokari? FDk, an ce mata mayaudara ne, to ai su ma mazan ba baya ba. Sai ga shi sun yaudare ni, don Allah ku ji tsoron ranar da amana za ta kama ku fa!

Daga Maimunat Umar Wushishi, 08063247134

Kira ga matasa

Sallama ga FDk, Dausayi kauna, ya ku samari ku iya soyyaya ta gaskiya da amana, za ta kai ku har ku san cewa ita soyayya ba ta tsufa sai dai masu yenta. Don haka ni ina shan romon soyayyata saboda na rike ta da gaskiya da amana

Daga Isma’il Mai Shadda Legas, 07032775928