Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Salah ya sake zama Gwarzon Dan Kwallon Afirka na 2018

A ranar Talatar da ta wuce ce Hukumar Kwallo ta Afirka (CAF) ta zabi Mohammed Salah, dan kasar Masar da yanzu haka yake buga wa kulob din Liberpool na Ingila kwallo a matsayin Gwarzon Dan Kwallon Kafa na Afirka na shekarar 2018.

Wannan ne karo na biyu a jere da dan kwallon yake lashe wannan gasa.

ADVERTISEMENT

Mohamemed Salah dai ya fafata ne a wannan gasa da takwaransa Sadio Mane da suke wasa tare a kulob din Liberpool na Ingila da kuma dan kwallon Arsenal dan kasar Gabon, Pierre-Emerick Aubameyang.

Shugaban Hukumar CAF Ahmad Ahmad ne ya sanar da haka a ranar Talata a Dakar, babban birnin kasar Senegal lokacin da hukumar ta gudanar da babban taronta na shekara-shekara.

ADVERTISEMENT

An zabi Salah ne saboda kokarin da ya yi a kulob din Liberpool a bara inda ya fi kowane dan kwallo yawan zura kwallaye a gasar.  Salah ya zura kwallaye 32 ne a raga wanda hakan ya sa ya zama dan Afirka na farko a tarihin gasar da ya taba samun irin wannan nasara.

A gasar ta bana ma, kawo yanzu Salah ya samu nasarar zura kwallaye 13 wanda hakan ya nuna idan ya ci gaba da nuna kwazo mai yiwuwa ya sake zama zakara.

Haka kuma wannan shi ne karo na biyar da dan kwallon Gabon Aubameyang yake shiga sahun wadanda suke fafatawa a wannan gasa.  Shi ne ya zama Gwarzon Dan Kwallon Afirka a 2015 da hakan ya nuna tauraruwarsa na ci gaba da haskakawa. Kawo yanzu ya zura kwallaye 15 a raga a gasar Firimiya ta Ingila a kulob din Arsenal.