✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallah bana:Raguna da rangwame amma ba kudi

Masu harkar sayar da dabbobi a Abuja sun koka kan karancin ciniki duk da rangwamen da suke da shi a bana idan aka kwatanta da…

Masu harkar sayar da dabbobi a Abuja sun koka kan karancin ciniki duk da rangwamen da suke da shi a bana idan aka kwatanta da bara. 

Wani dan kasuwa daga garin Mani a Jihar Katsina mai suna Malam Halidu Shu’aibu wanda ke sayar da dabbobi a kan babbar hanyar Kubwa zuwa Abuja, ya ce sun samu dabbobi da sauki tun a wurin sari a kasuwannin Mashi da Mai’aduwa da ke jiharsu ta Katsina sakamakon rashin manyan fataken dabbobi da ke zuwa can a bana, inda ya ce hakan ke jawo tashin farashin a baya. Sai dai kuma ya ce a wurin da suke sayarwa babu masu sayen dabbobin da yawa a tsakanin ma’aikatan gwamnati ko ’yan siyasa da suke bai wa jama’arsu.

“Ka ga kamar wannan babban rago a bara mun sayar da shi har Naira dubu 80 amma a bana ba ya wuce Naira dubu 60. Ga mu nan duk a zazzaune wurin ba hada-hada, amma a bara warhaka mun sayar da wanda muka kawo har mun je Kasuwar Deidei mun karbo nasu muna sayar musu,” inji shi. 

A babbar kasuwar dabbobi ta Abuja da ke Deidei, Sarkin Zangon Kasuwar Alhaji Muhammadu Sada Kusada wanda shi ma ya yarda da ra’ayin, ya ce a bana dabbobin sayarwa da aka kawo Abuja ba su da yawa idan aka kwatanta da bara, sannan ba a sayensu. Ya ce lamarin ya fi muni a kasuwarsu sakamakon yawaitar wuraren sayar da dabbobi a gefen tituna, maimakon shekarun baya inda kowa ke zuwa kasuwar tasu.

“Jami’an gwamnatin da ta gina mana wannan kasuwa ba sa yi mana adalci, su tura a sayo musu dabbobi a Arewa sannan daidaikunsu da ke saya su ma ba sa isowa wurinmu sai dai su tsaya a kan na titi, sai na can ya kare ne su masu sayarwa a wuraren su zo nan su sare namu,”  inji Sarkin Zangon.   

Daga Kalaba wakilinmu ya ruwaito cewa an samu rangwamen farashin dabbobi a Kasuwar Awaki ta Kalaba, Jihar Kuros Riba,  idan aka kwatanta da bara. 

Shugaban Kasuwar, Alhaji Muhammad Is’hak Ruba ne ya sanar da haka yayin hira da Aminiya, inda ya ce “Bana an samu saukin farashin raguna idan aka kwatanta da bara, raguna a bana suna yin sauki bana,” inji shi.

Shugaban Kasuwar ya ci gaba da cewa “Lamarin rayuwa wata rana idan an samu tsanani wata rana kuma sai a samu sauki. To wannan karo sauki ne Allah Ya kawo mana kuma alhamdulillahi mutane suna zuwa su saya duk da kukan rashin kudi da suke yi.”

Ya ce a gaskiya yana jin bana Kudu ta fi Arewa arha da kuma saukin saye raguna musamman a Kuros Riba. Ya ce saboda rahusan da ragunan ke yi masu saye domin layya suke zuwa. Ya ce “Ragon da muka sayar a bara kan Naira dubu 120 zuwa dubu 130 a bana yana kamawa daga Naira dubu 80 zuwa dubu 100, ka ga bana an samu rangwame,” inji  Isyaka  Ruba. 

Sai ya bayyana farin cikinsa kan janye musu masu karbar kudin shiga da haraji da jangali  da masu karbar ke ta kura musu suna zaluntarsu da kuma sanya su rika yin asara idan suka dauko dukiyarsu zuwa Kurmi domin sayarwa.

Daga Jihar Kano, wakilinmu ya ce rashin kudi a hannun mutane ya jawo rashin ciniki ga masu dabbobi kama daga shanu zuwa raguna da awaki da ake amfani da su wajen yanka Layya.

A kasuwar shanu ta dambatta wadda take ci ranar Lahadi, an yi ta komawa da shanu gida saboda rashin ciniki duk da irin arahar da suke yi. An sayar da manyan shanu daga Naira dubu 60 zuwa dubu 80, kuma har akwai na dubu 50, yayin da aka sayar da manyan raguna kan Naira dubu 50 zuwa dubu 75, sai kuma masu karamin kudi Naira dubu 20, sakamakon karancin kudi da jama’a suke fama da shi.

Wadansu manyan dillalan dabbobi a Kasuwar Badume da ke karamar Hukumar Bichi, Malam Sale Adamu Bagare da Abubakar Sulaiman Badume sun shaida wa Aminiya cewa a bana dabbobi ba sa tsada saboda rashin kudi a hannun jama’a. Sun ce duk da irin arahar da dabbobin suke yi, mutane sun rage yawan dabbobin da suke saye a lokaci irin wannan, inda suka ce wanda yake sayen raguna hudu zuwa biyar a bana bai fi ya sayi biyu zuwa uku ba. Su ma masu sayar da kaji sun koka da rashin ciniki duk da cewa kajin sun yi sauki  sabanin bara.

Kusan dukan kasuwannin da wakilinmu ya ziyarta lamarin haka ya kasance na rashin ciniki duk da arahar da dabbobin suke yi.

A Jihar Legas bincike da Aminiya ta gudanar ta gano cewa a bana an samu rangwame sosai a farashin ragunan Layya a kasuwar dabobi ta Sabo Ikorodu. Sarkin Kasuwar Alhaji Shitu ya shaida wa Aminiya cewa rago mafi karanci da za a iya yin Layya da da shi ana sayar da shi a kan Naira dubu 15 zuwa dubu 25 a kasuwar, yayin da akan samu madaidaici daga Naira dubu 35 zuwa dubu 50 sai kuma manyan raguna da akan samu na naira dubu 100 zuwa dubu 150. Sarkin Kasuwar ya ce an samu jinkirin masu zuwa sayen rago idan an kwatanta da bara, ya ce hasashe ya nuna cewa a bana mutane za su jinkirta har sai dab da Sallah domin samun karin rangwamen farashin ragon Layyar. 

A Kasuwar Alaba Rago inda a nan ne ake samun rago mafi girma a Jihar Legas, a bana babban rago mafi girma a kasuwar ya kama ne daga Naira dubu 150 zuwa sama, sai madaidaici da kan kama daga Naira dubu 45 zuwa 50. Sannan rago mafi karanci da za a iya yin Layya da shi yana kamawa daga Naira dubu 20 zuwa dubu 25. Alhaji Malami Ibrahim daya daga cikin shugabannin masu hada-hadar ragona a Kasuwar Alaba, ya shaida wa Aminiya cewa a bana sun samu karancin ciniki, inda mutane daidai ne ke zuwa kasuwar don sayan rago sakamakon lalacewar hanyoyin kasuwar. Ya ce sai dai masu sari kan je domin yin cinikin rago a kasuwar. Ya ce lalacewar hanyoyin Arewa ba su yi wani tasiri a farashin rago a bana ba, domin tsadar motoci daga Arewa ba su kai ga yadda ake biya a Kudu ba.