✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallamar Gulak darasi ne ga ’yan siyasa -Nyako

Gwamnan Jihar Adamawa Admiral Murtala Nyako ya bayyana sallamar mashawarcin Shugaban kasa kan al’amura siyasa Ahmed Gulak wanda dan jiharsa ne a matsayin abin tausayi…

Gwamnan Jihar Adamawa Admiral Murtala Nyako ya bayyana sallamar mashawarcin Shugaban kasa kan al’amura siyasa Ahmed Gulak wanda dan jiharsa ne a matsayin abin tausayi da zama babban darasi ga ’yan siyasa.
Gwamna Murtala Nyako wanda ya jajanta wa Barista Ahmed Gulak a kan sallamarsa da aka yi.
Nyako ya nuna rashin jin dadinsa game da yadda mutanen karamar Hukumar Gulak da garin Madagali inda tsohon mashawarcin ya fito suka nuna farin ciki game da faruwar hakan.
Gwamna Nyako ya cewa yadda mutanen karamar Hukumar Gulak suka yi farin cikin korar Ahmed Gulak daga aiki abin tausayi ne kuma hakan ya zama babban darasi ga ’yan siyasa musamman wadanda suke shirin shiga mulki.
Gwamnan wanda kakakinsa Malam Ahmed Sajoh ya yi magana a madadinsa ya ce ya kamata Gulak ya zama mai ba da shawara, amma sai ya zama mai bata sunan shugabanninsa a idon makiya. “Yau asalin mai yada labarai na fadar Shugaban kasa ya yi magana kuma ya kori Gulak har da watsa masa kasa a ido,” inji shi.
Bayanai sun ce wasu ’yan siyasa a jihar sun bayyana jin dadinsu da sallamar Gulak inda suka ce gwamnati ta yi daidai da ta kori Gulak.
A ranar Talatar da ta gabata ne Shugaba Jonathan ya sallami Barista Gulak, inda Kakakinsa Mista Reuben Abati ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter. Ya ce Shugaba Jonathan ya gode wa Gulak saboda gudunmawar da ya bayar ga gwamnatinsa.
A cewar Abati, nan gaba za a nada wanda zai maye gurbin Barista Gulak, sai dai sanarwar ta Mistta Abati ba ta yi karin haske a kan abin da ya sa aka sallami Gulak ba, amma masu sharhi kan al’amuran siyasa na kallon matakin a matsayin abin mamaki, ganin yadda Gulak ya takarkare yana kare gwamnatin Jonathan din kai da fata.