✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallar Bana: Farashin dabobbi na hauhawa a kasuwannin Kurmi

Binciken da Aminiya tayi a wasu kasuwannin dabobbi a jihohin Kurmi da suka hadar da Legas da Ogun da jihar Oyo da Osun da Ondo…

Binciken da Aminiya tayi a wasu kasuwannin dabobbi a jihohin Kurmi da suka hadar da Legas da Ogun da jihar Oyo da Osun da Ondo da Ekiti a bana farashin ragon layya yayi tashin goron zabi a yankin duk da karancin masu saye izuwa yanzu da kasuwar ragon layyar ke fama da shi.

Wasu daga cikin masu sana’ar sayar da dabbobin da wakilin Aminiya ya zanta da su sun alakanta tsadar ragon layya da rashin zaman lafiya a wasu jihohin Arewa wadanda suka hadar da Zamfara, Katsina da sauran su, suka ce akwai tarin fataken da ‘yan bindigar suka yi wa fashin a dazukan Zamfara da kewaye.

A jihohin Kurmin farashin karamin rago shi ne Naira dubu 40 zuwa 45 yayin da matsakaici mai dama-dama ke kai Naira dubu 50 zuwa 60 inda ake samun babban rago a Naira dubu 80 zuwa 100 inda akan sami bunsuru ko rago kafi zuru a Naira dubu 30 Bayaga hauhawar farashin ragon.