✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallar Bana: Raguna na araha masaya na kukan rashin  kudi

A yayin da jibi Lahadi ake sa ran gudanar da Idin Babbar Sallah, Aminiya ta bibiyi kasuwannin dabbobi daban-daban na kasar nan domin binciko yadda hada-hada…

A yayin da jibi Lahadi ake sa ran gudanar da Idin Babbar Sallah, Aminiya ta bibiyi kasuwannin dabbobi daban-daban na kasar nan domin binciko yadda hada-hada ke gudana, kasancewar layya na daya daga cikin ibadojin da al’ummar Musulmi ke gabatarwa a ranakun Idin.

A Abuja, Babban Birnin Najeriya, masu sayar da raguna da dabbobi sun bayyana cewa kasuwar Sallar bana  ta zo da saukin raguna da kuma cinikinsu. Wadansu da Aminiya ta zanta da su a kasuwannin dabbobi na wucin gadi a kan babban Titin Kubwa zuwa Zuba da ta dindindin da ke garin Deidei, sun ce hakan ya saba da ta Sallar bara, lokacin da suka fuskanci karancin kasuwa a ranakun farko.

Sun ce hakan bai rasa nasaba da biyan albashin ma’aikata gabanin shigowar tasu, sabanin bara, inda biyan albashin ya zo dab da Sallah kuma aka samu ingancin kasuwa a ranaku biyu kadai gabanin Sallah, inda suka koma gida da tarin ragunan da ba a saya ba.

Malam Mamuda Ado da ya kawo raguna a Titin Kubwa daga Karamar Hukumar Bunkure a Jihar Kano, ya danganta samun saukin dabbobin da yadda su kansu suka sayo tun daga kasuwannin kauye a Arewa, inda suke sari.

Shi kuwa Malam Manniru Isa Kwaranganba daga Karamar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato, ya ce saukin ragunan da kuma wadatarsu a kasuwannin da suke sari, ya faru ne sakamakon yadda masu kiwo suka gwammace sayar da dabbobinsu saboda yawaitar barayi da kuma tashe-tashen hankula a yankunan.

A zantawarsa da wakilinmu, Sarkin Zangon Deidei Alhaji Muhammadu Sada Kusada ya ce wani abu da ya kawo karin saukin dabbobin shi ne bude kan iyaka da ya ce an yi a bana, sabanin lokaci irin wannan a bara da aka rufe. Haka ya ce a bana an samu karuwar masu sayen raguna fiye da bara, inda ya ce yanzu ana shigowa kasuwannin ana sayen raguna kamar 15 zuwa 20. Sai dai ya ce hakan bai kai na shekarun baya ba kafin zuwan wannan gwamnati, inda ya ce ana sayen raguna 100 zuwa 200 don raba su ga jami’an gwamnati ko ’yan siyasa.

Shugaban masu sayar da raguna na kasuwar, Alhaji Abdullahi Abdulkadir da ke kawo ragunansa daga kasuwannin jihohin Borno da Yobe, ya yaba da dawowar wasu kasuwannin dabbobi a yankin a bana da a baya ya ce suka daina ci  sakamakon rashin  tsaro a lokacin. Ya ce daga cikin ragunan da ya kawo akwai kanana da kudinsu ya kama daga Naira dubu 35, yayin da a bangaren manyan na turke kuma, akwai har na Naira dubu 250.

Aminiya ta ziyarci kasuwannin dabbobi a Jihar Kano.

Duk da cewa rakumi yana cikin dabbobin da Allah Ya halatta a yi layya da shi amma jama’a da dama ba su fiye yin amfani da rakumi a layya ba. Sai dai a bana an samu canjin lamarin, inda bincike ya  gano cewa jama’a a Jihar Kano sun mayar da hankali wajen yin layya da shi. Lamarin da ake ganin ya faru ne sanadiyyar haurewar da farashin shanu ya yi.

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa farashin rakumi ya fi sauki fiye da kashi 20 a kan na saniya, domin rakumin da ake sayarwa a kan Naira dubu 100 to sai an sa Naira dubu 170 zuwa 200 idan za a sayi saniya makamanciyarta.

Malam Muhamamdu Rabi’u Sani, Shugaban Kasuwar Rakuma da ke Kofar Na’isa a Kano, ya bayyana wa Aminiya cewa  a yanzu haka sun fi cinikin rakuma fiye da na shanu. “A gaskiya zan iya cewa yanzu al’ummar Jihar Kano sun koma wa yin layya da rakumi fiye da shanu, lura da yawan cinikin da muke yi na rakuma wanda ya fi na shanu. Ina iya tunawa ko a bara mun sayar da rakuma fiye da shanu a wannan kasuwa. A yanzu ma haka abin yake, kafin a sayar da sa biyu an sayar da rakumi shida,” inji shi.

Da yake jawabi game da fitowar masu sayen dabbobin, Malam Rabi’u ya ce a gaskiya dama haka abin yake, domin ba a fiye sayen dabbobin ba sai  kwana biyu kafin layyar, don haka suna sa rai mutane za su zo sayen dabbobin kamar yadda aka saba.

A cewarsa wani karin dalilin da ya sa al’umma suka rungumi yin layya da rakumi shi ne yadda jama’a suka ilimantu a kan amfanin rakumi gaba daya ga lafiyar dan Adam. “Kin ga yanzu an gane cewa namansa ba ya cutarwa ko ga masu ciwon kafa. Haka kuma nononsa magani ne, jininsa ma idan aka tare shi daidai lokacin da aka yanka aka ba mai ciwon hakori ya kurkure bakinsa da shi to zai warke. Kai hatta fitsarinsa saye ake yi ana hada magunguna daban-daban da su,” inji shi.

Shi kuwa wani mai sana’ar fawa a Abbatuwa mai suna Ibarahim Mu’azzam, ya ce tun can asali  mutane ne ba su gane naman rakumi ba, domin a cewarsa ya fi na shanu kyau da lafiya. “Su mutanen da suke surutun naman rakumi yana da tauri sun jima suna cin naman rakumin ba tare da saninsu ba. Mahautanmu da yawa suna sayar da shi kuma babu wanda zai bambance maka tsakanin naman shanu da na rakuma sai wanda ya sani,” inji shi.

A ziyarar gani-da-ido da Aminiya ta kai Kasuwar Rakumar ta ga rakuma masu yawan gaske wadanda aka bayyana cewa dukkansu an sayar da su, ana  ajiyewa ne zuwa Ranar Sallah.

A Jihar Legas,  Aminiya ta ziyarci kasuwar Alabar Rago, a ranar Talatar da ta gabata, inda ta tarar da kasuwar makare da dabobbi da suka hada da raguna da awaki da shanu, kuma ta ga ana ci gaba da sauke dabobbi a kasuwar, yayin da ta iske masu saya daidaiku wadansu na saya wadansu na tayawa su wuce.

Mataimakin Shugaban Kasuwar Alabar Rago, Alhaji Bala Gwari ya shaida wa Aminiya cewa a Sallar bana da farko an yi hasashen  za a yi karancin dabobbi a kasuwannin Kurmi, sai dai kwana 7 zuwa 5 kafin watan Sallar sai al’amura suka sauya baki daya, inda aka yi ta samun tururuwar manyan motoci dauke da dabobbi daga Arewa da kasashen ketare da suka hada da Nijar da Kamaru da Chadi da Mali da Sudan.

Ya ce “Ana ciniki yadda ya kamata duk da kukan da ake yi na rashin kudi a hannun jama’a. Mu a nan ba mu ga hakan ba domin ana zuwa ana sayen dabobbin layya yadda ya kamata, ko a yau a gabana a nan kasuwarmu an zo an sayi rago daya a kan Naira dubu 600, an kuma sayi wani kan Naira dubu 350. An kuma sayi wani a kan Naira dubu  200, sannan akwai kanana sossai ’yan Naira dubu 20 zuwa dubu 25.”

A Jihar Ogun kuwa, Karar Basi ita ce kasuwa mafi girma ta dabbobi, inda nan ma fatake suke ta yi sam barka da kasuwar ba kamar yadda ake hasashe a baya ba.

Binciken da wakilinmu ya gudanar a garin Jos kan cinikin raguna, ya gano cewa a bana farashin dabbobi ya fadi kasa, sakamakon rashin kudi da mutane ke fama da shi.

A lokacin da wakilinmu ya ziyarci babbar kasuwar raguna ta ’Yan shanu da ke garin Jos, ya gane wa idanunsa tarin raguna amma babu masu saye.

Da yake bayani kan halin da ake ciki a kasuwar, shugaban kasuwar Alhaji Kawu Muhammed ya ce “Gaskiya kasuwar raguna ta bana ba ta kai ta bara ba wajen ciniki, domin a bara mun samu ciniki fiye da bana.”

Ya ce a bana masu kawo raguna su sayar da masu zuwa su saya sun ragu sosai, saboda halin da ake ciki na rashin kudi. Ya ce sakamakon rashin ciniki farashin raguna ya fadi, domin ragon da ake sayarwa a bara kan Naira dubu 200, a bana za a iya samunsa kan Naira dubu 150. “A bana idan mutum yana da Naira dubu 15 zai sami ragon da zai yi layya a wannan kasuwa. Amma bara sai mutum yana da dubu 20, zuwa dubu 25 kafin ya samu,” inji shi.

A Jihar Oyo kuwa, Aminiya ta ziyarci manyan kasuwannin dabbobi na Akinyele da Bodija da Aleshinloye, inda wakilinmu ya ga sun cika makil da raguna da ’yan kasuwa suka yi fataucinsu daga sassan Arewa. Sai dai a binciken nasa ya gano cewa rashin kudi a hannun mutane ya sa wadanda suka saba shiga cikin kasuwanni kwana biyar kafin ranar Sallah domin sayen ragunan layya sun yi nesa-nesa da  kasuwannin.

Wadansu magidanta ’yan kasuwa da ma’aikatan gwamnati sun yi wa Aminiya bayanai daban-daban. Alhaji Uzairu Maimota ya ce, “Shekara 19 da wucewa ke nan da na fara yin layya, a kowace shekara ina sayen raguna biyu ba tare da ganin tsadarsu ba, domin Allah Ya wadata ni da kudin da zan iya saya. Amma a bana duk da alamar farashin raguna ya yi sauki, ina ganin ba zan iya sayen rago ko daya ba domin babu kudin sayen kuma babu masu sayen kayan da muke sayarwa.”

Alhaji Abdulfatah Aremu kuwa cewa ya yi, “Tun makon jiya aka biya mu albashi amma mun kashe kudin duka, babu sauran ko kwabo saboda haka ba zan iya sayen rago a bana ba.”

Ita kuwa Hajiya Mulikat Balogun cewa ta yi, “Shekaru da yawa da suka wuce ni ce nake sayen ragon da muke yin layya duk shekara. Ina samun kudin sayen rago ne daga ribar da na samu daga dafaffen abinci da nake sayarwa ga mutane a kan hanya. Dole ne mu yi hakuri da yin layya a bana, domin babu jari balle mu samu ribar sayen rago a bana.”

A Jihar Sakkwato ma Kasuwar Dabbobi tana gudana, inda wakilinmu ya ruwaito cewa ragon Naira dubu 30 ko marakin Naira dubu 250 ne kadai ke isa yin layya a bana, kamar yadda Kungiyar Masu Sayar da Dabbobi a Jihar ta bayyana.

“A bana ba a samu wani bambanci  sosai ba a farashin raguna, yadda mutane suka sani ne, ragon da ke layya a nan wajenmu farashinsa daga  Naira dubu 30 ne zuwa sama har zuwa Naira dubu 100 da kari akwai,” inji Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Raguna da Awaki ta Sakkwato, Alhaji Isa Bello Unno Sabon Birni.

Alhaji Isa ya ce a shekara uku da suka gabata kasuwanci ya canja ba kamar shekarun baya ba da suke fara hada-hadarsu tun Sallah saura kwana 30, amma yanzu mako daya ne suke ciniki sosai. Ya yi kira ga masu sayar da dabbobi a ko’ina suke su sassauta wa masu saye domin ibada ce za su yi.

Ya yi godiya ga Gwamnatin Sakkwato kan filayen da aka ba su suka gina shaguna a kasuwar. Ya kuma musanta zargin da ake yi, cewa gwamnati ta karbe filayen ne daga wasu ta bai wa kungiyar. “Duk wanda ke wannan maganar harka ce ta son rai. Fili na gwamnati ne aka rika zuba shara wurin, muka nemi Gwamna Tambuwal ya ba mu ya aminta aka raba wa mutanen kungiyarmu suka gina shaguna ana kasuwanci. Bayan karamin asibitin dabbobi da aka yi mana, akalla muna tare da likita biyar a nan da suke duba mana dabbobinmu, duk mai wata cuta ana fitar da ita ta sha magani.”

Wakilinmu ya kalato daga bakin mutane a Jihar Sakkwato, cewa dabbobi suna tsada a bana.

A Jihar Kuros Riba kuwa, Aminiya ta gano cewa an samu tangarda wajen shigowa da ragunan domin masu saye. A Kasuwar Dabbobi da ke Layin Mary Slessor a Unguwar Hausawa Layin Bagobiri, babu alamun raguna na sayarwa da aka kawo, sai dai daya daga cikin ’yan kasuwar, Alhaji Is’haka Ruba ya ce dalilan da suka sanya bana aka samu jinkirin zuwan dabbobin Kalaba shi ne, “Ba mu samu mota daga Arewa ba da za ta kawo mana su, amma muna sa ran wata motar za ta taso daga Jigawa da raguna kuma muna sa rai koda kasuwar za ta kankama watakila sai daga ranar jajibiri zuwa bayan Sallah da kwana daya ko biyu,” inji shi.

Wakilinmu ya leka kasuwar sayar da raguna da ke Layin Barracks a Kalaba, inda Malam Mukhtar Ahmad Abubakar ya bayyana yadda kasuwar dabbobin ke gudana. “A bana nan Kalaba ba mu kawo raguna irin wadancan masu tsada ba, muna duba yanayi na wuri ne kafin a kai musu raguna saboda haka nan mafiya yawan farashin rago ya yi yawa a samu na Naira dubu 160 zuwa 150. Mafi kankantar farashi a kasuwar nan ba ya wuce Naira dubu 30,” inji shi.

Wata matsala da dan kasuwar ya koka da ita da ya ce tana ci musu tuwo a kwarya ita ce ta karancin kudi da mutane ke fama da shi amma duk da haka ana zuwa ana saye jifa-jifa.

A kasuwar wakilinmu ya ci karo da wani da ya zo sayen rago mai suna Umar Jibrin Darki wanda ga alama farashin ragunan ya fi karfin aljihunsa, inda ya fara ciniki ya hakura. Da aka tambaye shi ko sai ya ce, “Cinikin bai kaya ba, ba ma na tunanin zai kaya saboda su masu ragunan suna sa tsada kuma yadda al’amura suke a yanzu wanda ya saba sayen raguna uku ya yi layya amma yanzu saboda yanayin yadda shekarar ta zo wallahi ba mamaki bana daya ma ba zai samu ba.”