Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Sallar idi: Jan kunnen Limamin Zazzau ga shugabanni

Sallar idi: Jan kunnen Limamin Zazzau ga shugabanni

Dubban al’ummar Musulmi ne suka halarci raka’oi biyu na sallar idin layya a Masallacin Idi na kofar Doka, Zariya.

An tayar da sallar ce da misalin karfe 9 na safe, bisa jagorancin Babban Limamin Zazzau, Shaikh Dalhatu Kasimu Yero.

A cikin hudubar sa limamin na Zazzau ya hori daukacin al’ummar Musulmi su koma ga Allah tare da gyara dabi’u domin samun tsira a nan duniya da gobe alkiyama.

Ya ce, ba za’a taba samun dawwamammen zaman lafiya ba sai al’umma ta rungumi kaunar juna da yi wa juna fatan Alheri da kuma tausaya wa na kasa.

Kuma ya bukaci shugabanni su ji tsoron Allah a jagorancinsu, kuma su sani Allah Zai tambaye su a kan dukkanin abubuwan da suka aikata na Alheri ko sharri.

Da ya juya ga mabiya kuwa, Shaikh Dalhatu Kasimu, kira ya yi gare su da su ci gaba da yi wa shugabanni addu’a tare da fatan alheri da kuma bin umarninsu matukar bai saba wa Allah Mahalicci ba.