Da Dumi Dumi

Sallar Idi: Sarkin Zazzau Ya Nesanta Kansa da Sanarwar Limamin Masarauta

Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris
Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris

Masarautar Zazzau a jihar Kaduna ta nesanta kanta da sanarwar da yawunta babban limamin masarautar ya bayar na cewa za a yi Karamar Sallah a ranar Asabar 23, ga watan Mayu.

Kwamitin ganin wata na masarautar ya ce bai ba da umarnin jama’a su ajiye azumin watan Ramadan a ranar Asabar 23 ga watan Mayun shekarar 2020 ba.

“A saboda haka Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idri  ke kira ga jama’ar Musulmi a masarautar su bi umarnin Mai alfarma Sarkin Musulmi wanda shi  Allah Yaa dora wa hakkin  sanar da ganin watan Ramalan da Shawwal,” inji Kwamitin.

Shugaban Kwamitin Alhaji Ibrahim Muhammad Aminu, Wazirin Zazzau ya bayyana hakan a daren Juma’a.

Sanarwar da ya rattaba wa hannu, ta ce ce sanarwar da Limamin Zazzau Malam Dalhatu Kasimu Imam ya bayar, ba da sahalewar masarautar Zazzau ba ne.

ADVERTISEMENT

A bana Birnin Zariya da ma kafatanin jihar Kaduna ba za a yi sallar Idi ba, a yunkurin da gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufa’i yake na kare yaduwar annobar coronavirus a jihar.

A daren Juma’a ne Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar cewa za a cike azumin Ramadan 30 saboda ba a samu rahoton ganin jinjirin watan Shawwal

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya