Da Dumi Dumi

Salman Khan na fuskantar tuhumar kisan kai

A Lahadin da ta gabata ce wata kotu a birnin Mumbai ta zartar da hukuncin cewa za ta tuhumi jarumin fina-finan Indiya, Salman Khan da laifin kisan kai, kasancewar ya banke wasu mutane da motarsa a yayin da ake zargin yana kan tukin gangaci.
dan fim din dai ya banke mutum hudu ne da motarsa shekaru goma da suka gabata, inda uku suka samu munanan raunuka, daya kuma ya mutu.
A can baya kafin a canza tuhumar, an tuhume shi ne da caji mai sauki, wanda hukuncinsa ba zai wuce daurin shekaru biyu ba a gidan yari, amma a wannan sabon caji, madamar an kama shi da laifi, za a iya yanke masa hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari.
Wannan hukunci dai ana ganinsa ne a matsayin wanda ya gigita duniyar fina-finan Indiya, musamman ganin cewa Salman Khan na daya daga cikin jiga-jigan ’yan wasan da ke fantamawa a wannan zamanin.
Jarumin dai ya share shekaru 25 da fara harkar fim, inda ya fito cikin manyan fina-finai sama da guda 90.
Kamar yadda mai shari’a ya zartar, za a fara sauraren shari’ar ta Salman a ranar 19 ga watan gobe, idan Allah Ya kai mu.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya