Sama da ’yan Najeriya miliyan 60 ba su iya rubutu da karatu ba

Hukumar Yaki da Jahilci ta Najeriya ta ce sama da mutanen Najeriya miliyan 60 ba sa iya karatu da rubutu a kowane irin harshe.

Babban Sakataren Hukumar, Farfesa Abba Abubakar Haladu ne ya bayyana hakan a lokacin taron zantawa mai taken “Ilimi da amfani da harsuna da yawa: Ginshikin Cibana Kasa mai Dorewa a Abuja.

Farfesa Haladu ya kara da cewa duba ya dubban matasan da suka bar makaranta da kuma yawan mutanen Najeriya, dole abin ya shafi miliyoyin mutane.

Ya ce idan har Najeriya ta so cimmawa burin cigabanta, dole mutanenta, mata da maza, yara da manya a duk inda suke su koyi akalla karatu da rubutu.

A nasa jawabin, Ministan Ilimi, Adamu Adamu wanda ya samu wakilcin Minista a Ma’aikatar Ilimi Emeka Nwajiuba cewa ya yi, “yana matukar muhimmanci mu yi gaggawar canja yanayin kididdigar nan da ke nuna yawan mutanen da ke barin makaranta da kuma yawan rashin ilimi a tsakanin matasa da manyan da kuma rashin abubuwan da ake bukata wajen koya da koyar da karatu da sauransu.”

ADVERTISEMENT
Share