Gwamnan Jihar Legas, Mista Babatunde Raji Fashola ya kaddamar da fitilun titi a tsohuwar gadar Carter Bridge, wadda ta hada dukan sassan Legas, wato Lagos Island da Lagos Mainland, wadda aka gina tun a shekarar 1901 kuma a shekarar 1973 aka sake mata kwaskwarima.
An samar da turakun fitilu har 412 daga farko har karshen gadar, baya ga wadanda aka samar a gefen masu tafiya da kafa da kuma hasken da ke raba titin, lamarin da ya haskaka duk sassan Ijora Olopa da Iddo Terminus da EbutewEro.
A jawabinsa lokacin kaddamar da fitilun, Gwamna Fashola ya ce samar da wadataccen hasken lantarki a sassan jihar na daya daga cikin abin da gwamnatin jihar ta yi wa jama’ar alkawari, duk da yake ba aikinta ba ne. Ya ce samar da fitilun, zai agaza wajen rage yawan barayi, kana ya samar da karin zirga-zirgar ababen hawa a yankunan.
Gwamna Fashola ya ce samar da wadannan fitilu, shi ne aiki irinsa na farko da hukumar samar da lantarki ta jiha mai zaman kanta ta samar, kuma tuni har an fara aikin fadada shi zuwa wurare kamar asibitoci hudu da ke yankin da makarantu 14 da wuri biyu na samar da ruwan sha ga wani sashen jihar da kotuna 2 da kuma titi mai tsawon kilomita 30.
Gwamnan ya ce gwamnati ta gama nata, yanzu ya rage ga mutanen gari, musamman wadanda ke makwabtaka da wadannan wuraren su sa ido su kula da shi tamkar nasu.
Ya ce daga cikin abubuwan da ke kawo lalacewar kayan gwamnati shi ne yadda wasu ’yan kasa kan rika yi masa rikon sakainar kashi ta nuna halin ko-oho. Ya kamata a ce an wuce wannan yanayin domin al’umma kodayaushe kara wayewa take yi. Don haka ya kamata jama’a su kula da wadannan fitilu, wadanda da kudinsu ne aka samar da su.
Samar da fitilu a manyan titunan Legas na rage yawan barayi Inji Gwamna Fashola
Gwamnan Jihar Legas, Mista Babatunde Raji Fashola ya kaddamar da fitilun titi a tsohuwar gadar Carter Bridge, wadda ta hada dukan sassan Legas, wato Lagos…