✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Samar da sabon iri: Manoma a Zamfara za su koma noman auduga

Manoman Auduga a Jihar Zamfara sun ce a shirye suke su koma ga noman auduga a jihar bayan da wani kamfanin samar da inganttacen irin…

Manoman Auduga a Jihar Zamfara sun ce a shirye suke su koma ga noman auduga a jihar bayan da wani kamfanin samar da inganttacen irin auduga mai suna Mahyco Cotton Hybrids Bollgard 2 ya samar musu da igantaccen iri domin gwaji a gonakinsu.

Sabon irin mai suna Mahyco 567 BG2 da Mahyco 571 BG2 tsutsar  da ke lalata yabanyar auduga da ake kira bollworm ba ta iya illata shi, kuma yana bada amfani mai yawa idan aka kwantanta da nau’o’in irin auduga da manoma suke shukawa a baya.

Shugaban Bunkasa Sashin Kasuwanci na Kamfanin Malam, Yusuf Hamza ya ce kimanin manoma 300 ne aka ba irin suka shuka a bana kuma sun yi mamakin yadda irin ke samar da amfani mai yawan gaske ga shi kuma kwari ba sa iya lalata shi.

Manoman sun shaida wa wakilinmu a wani taro da  Shugaban Bunkasa Kasuwanci na Kamfanin Mahyco  Cotton Hybrids Bollgard 2, Malam Yusuf Hamza ya jagoranta a gonar wani manomin auduga a kauyen Rugar Na-Ali da ke Karamar Hukumar Tsafe cewa sun ga fa’idar shuka ingantaccen irin kuma za su ci gaba da shuka shi a kowace damina.

Wani manomin auduga mai suna, Yahaya  Muhammad Bilbis, ya shaida wa Aminiya cewa a baya sun guje wa noman auduga ce saboda rashin ingantaccen iri. To amma yanzu an kawo sauyi kan yadda manoma ke kallon harkar samar da auduga a kasar nan.

“Ba ma kawai rashin samar da iri mai kyau ne matsalar ba, tsutsar da ke mamaye yabanyar auduga ta lalata ta, ta dade tana ci wa manoman auduga tuwo a kwarya. To amma muna shirin dawowa ga noman auduga haikan saboda sauyin da aka kawo.

“Na shuka irin na Mahyco 567 BG 2 kuma na ga bambanci kwarai da gaske idan aka kwatanta da abin da irin auduga na baya ke samarwa, auduga ta samu. A wuri kadan manomi zai samu auduga mai yawa kuma tsutsa ba za ta cutar da ita ba,” inji shi.

Ya ce, “Idan da mun san wannan irin zai samar da auduga mai yawa kamar haka da mun ninka abin da za mu iya samawar na audugar a bana. To amma duk da haka za mu kara fadada noman auduga a badi idan Allah Ya kai mu,” inji shi.

Wani manomi mai suna Alhassan Unguwar Chida, shi ma ya ce bai taba ganin irin auduga mai  kyau kamar Mahyco 567 BG2 da kuma Mahyco 571 BG2 kuma nan gaba zai zama irin da zai rika amfani da shi a gonakinsa.

“Idan yanzu akwai irin audugar a kasuwa to kuma akwai masayansa. Don haka muna rokon hukumomi su samar da shi da yawa ga manoma. Don a cikin mako daya kacal za a iya hada kudinsa, domin mun shuka shi mun kuma ga fa’idarsa.

Babbar matsalar da ke addabar manoman auduga ba ta wuce rashin irin mai kyau ba kuma yanzu sannu a hankali ana manganin wannan matsala. Domin ana kokarin farfado da noman auduga ta hanyar maganin ainihin ciwon da ke damun manoman,” inji shi.

Alhaji Sani Dahiru shi ne Babban Manajan Daraktan Kamfanin Intaginnery kuma Shugaban Kungiyar Manoman Auduga ta Jiha Zamfara, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da  gwamnatocin jihohi su hada hannu da Kamfanin Mahyco domin samar da irin ga manoma.

Malam Yusuf Hamza, ya ce sabon irin na Mahyco yana iya samar da audugar da za ta kai tan 4.1 zuwa tan 4.4 a hekta daya idan aka kwatanta da kilo 250 zuwa kilo 900 da irin auduga na baya ke samar wa manoma a hekta daya .

Ya kara da cewa amfani da sabon irin zai sa tsutsar nan mai suna bollworm ta zama tarihi. Kuma manoma su samu amfani mai yawa a wuri kadan. Don haka manoman da aka yi wannan shiri dominsu, su ne za su ci moriyarsa.