Categories: Kasuwanci

Samar da tashar jirgin kasa a Rigasa alheri ne – ’Yan kasuwa

Wadansu ’yan kasuwa da ke harhar kasuwanci a tashar jirgin kasa ta Rigasa a Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna sun bayyana samar da tashar jirgin a matsayin alheri gare su da garin Rigasa.

A cewarsu, tunda aka kafa tashar kusan shekara uku harkokin kasuwanci da tattalin arzikin yankin sai ci gaba suke yi.

ADVERTISEMENT

Wadansu daga cikin ’yan kasuwar da Aminiya ta zanta da su sun nuna irin alherin da suke samu tun lokacin da jirgin ya soma aiki.

Sabon Shugaban ’Yan Kasuwar Tashar Jirgin Kasa ta Rigasa Malam Nasiru Adamu ya ce hakika harkokin kasuwanci na bunkasa a tashar saboda yawan jama’a da ke shege da fice a tashar a kullum.

ADVERTISEMENT

Ya ce masu harkoki a tashar sun hada da ’yan Keke NAPEP da masu hayar motoci da masu duba motocin matafiya da masu sayar da abinci da masu shayi da masu sayar da kayan masarufi da sauransu.

“Zan iya fada maka cewa duk wanda yake kasuwanci ko sana’a a wajen nan yana jin dadi domin mu a gare mu kafa wannan tashar jirgi alheri ne babba. Domin al’ummarmu da ke harkokinsu a nan na farin ciki.

Wannan jirgi ya kawo mana alheri sosai domin muna ci gaba da gudanar da kasuwancinmu cikin kwanciyar hankali,” inji shi.

Malam Nasiru Adamu ya bukaci gwamnati cewa duk lokacin da ta shirya gina shaguna na dindindin a wajen akwai bukatar ta damka wa shugabannin ’yan kasuwar tashar alhakin raba wa ga mambobinsu domin su suka fi sanin wadanda ke kasuwanci a wajen a yanzu.

Malam Haruna  Rigasa daya daga cikin shugabannin Kungiyar ’Yan Kasuwar da ke rike da mukamin Sakataren Kudi kuma yake cikin masu kula da motocin matafiya a tashar cewa ya yi:

“A shekarun baya sana’ar tukin mota nake yi amma saboda rashin motar na fara aiki a nan a matsayin daya daga cikin masu lura da motocin matafiya. Gaskiya harkokin kasuwanci a nan sai hamdala. Domin a yanzu komai na tafiya yadda ya kamata musamman a bangaren kasuwanci da sana’oi a tashar. Sai dai kiranmu akwai bukatar hukumomin tashar su dauki ’yan asalin Rigasa aiki ko da na sayar da tikiti ne. Yin hakan zai rage marasa aikin yi a garin Rigasa,” inji shi.

Malam Yakubu Abubakar Kubarachi wanda ke sayar da kayan masarufi a tashar kuma tsohon Shugaban ’Yan Kasuwar Tashar ya ce ba su fi mutum biyu da suka fara harka a tashar ba, amma yanzu sun kai sama da mutum 100 da ke kasuwanci a wajen.

“Wannan ya nuna cewa harkoki na tafiya yadda ya kamata domin ba mu fi mu biyu da muka fara harka a wajen ba amma ga shi yanzu mun kai sama da mutum 100 da ke cin abinci a wajen nan.

Saboda haka tashar alheri ne gare mu sannan ga shi tana kara fahimta a tsakanin mu Musulmi da wadanda ba Musulmi ba, domin a kullum suna shigowa nan don  sayayya, wanda hakan na kara kawo fahimtar juna. Idan ka zagaya cikin kasuwar za ka ga yadda jama’a ke tururuwa zuwa yin sayayya ko cin abinci kafin jirginsu ya tashi zuwa Abuja,” inji shi.

. .

Recent Posts

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

6 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

6 hours ago

Matashin da ke sace kudin coci ya shiga hannu

Wani matashi da ake zargi da sace kudin da ake tarawa na sadaka a cocin "Divine church of God" a…

7 hours ago

‘Yan Sanda sun bada belin Malam Niga a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayar da belin Malam Lawal Yusuf Muduru da aka fisani da Malam Niga wanda…

19 hours ago

An yi garkuwa da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da yin garkuwa Kwamandan shiyyar Karamar Hukumar Suleja kuma Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda ACP Musa…

1 day ago

An gano zakin da ya tsere daga gidan zoo na Kano

Bayan shafe daren jiya ana neman wani rikakken zaki da ya kufce daga gidansa a gidan namun daji na Kano,…

1 day ago