✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Samun ‘yanci kananan hukumomi zai raya kasa – Namashaya

Alhaji Umaru Namashaya Diggi, shi ne Shugaban Karamar Hukumar Kalgo da aka zaba a karkashin Jam’iyyar APC. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya ce bai wa…

Alhaji Umaru Namashaya Diggi, shi ne Shugaban Karamar Hukumar Kalgo da aka zaba a karkashin Jam’iyyar APC. A tattaunawarsa da wakilinmu, ya ce bai wa kananan hukumomi cin gashin kansu zai raya yankunan karkara:

Me za ka ce kan bai wa kananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu?

Na ji dadin wannan tambaya, kuma ka sosa mini inda ke yi mini kaikayi. Babu shakka bai wa kananan hukumomi ’yanci ta ba wa kananan hukumomi damar samun bunkasa, kuma hakan zai taimaka wa al’ummar kasar nan. Domin idan aka duba Gwamnatin Tarayya gwamnati ce mai zaman kanta, haka gwamnatin jiha, sannan  gwamnati karamar hukuma kuma  a nan ne talakawa suke zaune kuma ita ta fi kusa da al’umma.To don haka ne Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya yi kokarin ganin kananan hukumomin na da ’yancin cin gashin kansu, don samun damar yi wa al’ummar karkara ayyukan raya kasa. Shugaban Kasa ya yi hangen nesa sosai wajen ba kananan hukumomin kudadensu kai-tsaye.

Ganin Gwamanatin Tarayya ta fara ba ku kudadenku wadanne kudirori kake da su ga al’ummarka?

A takaice ina da kudirori biyar, na farko kamar yadda muka sani ne cewa duk wani dan Karamar Hukumar Kalgo, babban abin da ya dogara das hi, shi ne noma. Don haka ina da kudirin idan Allah Ya yarda za mu bunkasa harkokin noma, kuma za mu cire siyasa wajen rabon takin zamani ga manoma, domin manomi abin da yake bukata shi ne a ba shi taki da ingantaccen iri a lokacin da ya dace, walau noman rani ne ko na damina. Sannan ga maganar ilimi, duk wata al’umma da ta samu ci gaba a duniya za a samu cewa ilimi ne jigon haka, don haka za mu yi kokari mu kyautata harkokin ilimi tun daga makarantun firamare  zuwa manyan makarantun da muke da su, sai maganar kiwon lafiya nan ma za mu tabbatar cewa mun inganta asibitocinmu, ga maganar matsalar ruwa sha da muke fama da ita musamman  da rani, bugu da kari za mu bunkasa harkokin kiwo. Ko a kwanan nan Uban Kasar Diggi Alhaji Abubakar Atiku Muhammad da Karamar Hukumar Kalgo mun kafa kwamiti a karkashin jagorancin Jami’in Kula da Aikin Gona don ya gano matsalar da ke haddasa rikicin manoma da makiyaya a yankin, don a  samu zaman lafiya kuma a ba kowa hakkinsa.

Me za ka ce ga Gwamnatin Jihar Kebbi kan rashin gudanar da ayyukan raya kasa a yankinku?

To a halin gaskiya mu a yankinmu na Diggi babu abin da ke ci mana tuwo a kwarya illa abu biyu; na farko hanyar da ta tashi daga garin Jeji zuwa Diggi ta zarce zuwa Keta, wadda idan Gwamnatin Jihar Kebbi ta gina mana to a gaskiya ta yi mana komai. Kuma ina kara kira ga Gwamnatin Jiha ta dubi wannan yanki namu na Diggi da idon rahama, domin a wannan yankin ba mu da wani mai rike da mukami a gwamantin, walau Darakta ko wani babban mukami, sai ni kadai Shugaban Karamar Hukuma. Kuma duk wanda Jihar Kebbi ya san cewa al’ummar Karamar Hukumar Kalgo sun ba da gaggarumar gudunmuwa lokacin zaben Shugaban Kasa da na Gwamna, saboda haka ya kamata Gwamna Abubakar Atiku ya ba al’ummar wannan yanki mukamai domin a dama da su.