✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanata Ahmad Lawan ya dace  maye gurbin Saraki – Danmalikin Kebbi

Tsohon Ma’ajin Jam’iyyar APC na Jihar Kebbi Alhaji Musa Abubakar Danmalikin Kebbi, ya ce Sanata Ahmad Lawan ne ya fi dacewa da Shugabancin Majalisar Dattawa.…

Tsohon Ma’ajin Jam’iyyar APC na Jihar Kebbi Alhaji Musa Abubakar Danmalikin Kebbi, ya ce Sanata Ahmad Lawan ne ya fi dacewa da Shugabancin Majalisar Dattawa. Alhaji Musa Abubakar wanda har ila yau shi ne Shugaban Kungiyar Goyon Bayan Buhari, ta Buhari Support Organization a Jihar Kebbi  ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa da ke Yari Plaza a  Birnin Kebbi, inda ya nuna goyon bayansa ga Sanata Ahmad Lawan daga Jihar Yobe, wanda ya ce ya cancanci samun wannan matsayi don maye gurbin Shugaban Majalisar mai barin gado Sanata Bukola Saraki.

Alhaji Musa Abubakar ya kara da cewa abin farin ciki ne yadda Jam’iyyar APC ke da mafi rinjaye a majalisar, kuma suna goyon bayan Sanata Ahmad Lawan ya shugabanci majalisar  ce saboda kwarewa da hazakar da yake da ita.

Danmalikin na Kebbi ya ce tun da aka dawo mulkin dimokuradiyya a 1999 yankin Arewa maso Gabas bai taba samun Shugaban Majalisar Dattawa ba.

Danmalikin ya nemi dukan sanatocin Jam’iyyar APC, su jajirce don ganin Sanata Ahmad Lawan ya zama Shugaban Majalisar Dattawa domin ci gaban kasar nan.

Ya kuma kara jawo hankalin sanatocin da kada su sake maimaita irin kuskuren da suka yi a baya na zaben bara-gurbi a matsayin shugabannin majalisar.