✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanata Al-Makura ya bukaci gwamnonin Arewa su dawo da kwalejojin horar da malamai

Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa kuma sanata mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Kudu Umaru Tanko Al-Makura ya bukaci Gwamnatin Tarayya da duk gwamnonin jihohin kasar nan…

Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa kuma sanata mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Kudu Umaru Tanko Al-Makura ya bukaci Gwamnatin Tarayya da duk gwamnonin jihohin kasar nan da su gaggauta dawo da makarantan horar da malaman makarantun firamare da ake kira Gobernment Teachers College jihohinsu.

Sanatan ya yi wannan kira ne a jawabinsa na wajen babban taron kungiyar tsofaffin daliban tsohuwar Kwalejin Horar da malaman makarantun firamare na gwamnati da ke garin Keffi a ranar Litinin da ta gabata.

“A gaskiya wasu shirye-shiryen gwamnatocinmu suna hana ruwa gudu a harkokin iliminmu, musamman na horarwa don galibin shirye-shiryen ba sa ba da fifiko ga fannin kamar yadda ya dace kuma ba sa la’akari da yawan makarantun firamare a kasar nan wadanda ba su da kwararru da ishesun malamai. Ko mun ki ko mun so dole ne mu dawo da shirye-shiryen gwamnati na shekarun baya yadda muka taso muka gani a fannin iliminmu, idan muna so mu daukaka darajar fannin.

“Shi ya sa a yau yawancin malaman da suka kammala kwalejin ilimi masu takardar koyarwa ta NCE ba su yi kusa da tsofaffin malamanmu na da ba a bangaren kwarewa da sanin aiki da sauransu. Shi ya sa nake so inyi amfani da damar nan in yi kira ta musamman ga duka gwamnoninmu da Gwamnatin Tarayya su gaggauta dawa da shirin don sauya fasalin kananan makarantunmu”.

Daga nan sai ya jinjinawa kungiyar tsofaffin daliban Kwalejin Horar da malaman dangane da shirya taron, inda ya ce hakan yana kara dankon zumunci

Tun farko a jawabin Shugaban Kungiyar a jihar, Alhaji Abubakar Usman Sandaji ya bayyana dakatar da shirin horar da malaman kananan makarantun kasar nan da aka yi a shekarar 1994 a matsayin babban kuskure da rashin hangan nesa daga wasu shugabannin kasar nan inda ya bukaci Gwamnatin Tarayya da sauran gwamnatoci da dawo da shirin a duka kananan hukumomi 774 da ke kasar nan.