Aminiya

Sanata Ali Wakili: Garma ta karye da sauran aiki

Aranar Asabar da ta gabata ce 17 ga Maris, muka wayi gari da labarin rasuwar Sanata Malam Ali Wakili na mazabar Bauchi ta Kudu a karkashin Jam’iyyar APC. Rasuwar da ta girgiza masoya da magoya baya da kuma abokan adawar siyasar marigayin.

Marigayi Malam Ali Wakili wanda ya rasu yana da shekara 58, kuma ya bar matan aure biyu da ’ya’ya 11, mutum ne da aka shaide shi da cewa ba ya magana biyu, ba ya da tsoro ko shakkar bayyana abin da ya yi imani cewa shi ne gaskiya.

Ina daya daga cikin mutanen da za su iya cewa wani abu kan wannan bawan Allah wanda muka fara hulda kai-tsaye fiye da shekara 10 da suka gabata.

Yadda muka fara hulda da marigayin:

ADVERTISEMENT

Duk da cewa na san Malam Ali Wakili tun yana aikin Kwastam amma wata harka ba ta taba shiga tsakaninmu ba, sai bayan da aka yi masa ritaya daga aiki. Wata ranar Juma’a ya kira ni a waya ya tambaye ni cewa ina nake?  Na ce masa ina hanyar zuwa Bauchi, shi ma ya ce ga shi nan ya taso daga Kano yana bukatar mu hadu. Ya yi min kwatancen gidansa na je, ina zuwa ya ce dama kai ne aka ce in nema? Ai na san ka. Nan dai muka tattauna, sannan ya bayyana min cewa yana sha’awar shiga siyasa don haka yana son tattauna al’amuran da suka shafi jihar da kasa da jaridar Aminiya. Babban abin da ya fi burge ni game da shi, shi ne yadda yake haba-haba da mutane. Wani abu kuma game da Sanata Ali Wakili shi ne ya san muhimmancin watsa labarai kuma yana daukar ’yan jarida tamkar abokai cikin mutuntawa da girmamawa.  

Tun daga wancan lokaci, daga lokaci zuwa lokaci yakan nemi mu tattauna, ko in wani abu ya taso in nemi shi domin jin ta bakinsa.

Lokacin da suka cika kwana 100 a Majalisar Dattawa kuma ake tsakiyar zargin sanatoci da zame kafar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, musamman bayan da suka zabi shugabannin majalisar wanda bai yi wa Jam’iyyar APC da wadansu dadi ba, ya kira mu ni da abokin aikina na Daily Trust, Hamza Idris inda ya mayar da martani, yana cewa shi da Shugaba Buhari babu shamaki a tsakaninsu, bai taba gaya musu ga wanda yake so zu zaba a matsayin Shugaban Majalisa ba, kuma duk abin da ya nema daga majalisa za su tabbatar ya samu don ci gaban kasa.

Ganawarmu ta karshe:

Sai dai abin mamaki a karshen watan Janairun bana, sai ya bugo min waya, ya ce “Baba Saleh, (sunan da ya fi kira na da shi,) abubuwa suna ta faruwa a kasa ba ka neme ni ba?” Sai na ce ya ba ni lokacin da yake so mu gana. Allahu Akbar! Ashe wannan ganawa ita ce za ta kasance ta karshe a tsakanina da shi.

Na je gidansa na Gwarimpa a Abuja, kuma ina zuwa aka sanar da shi, ya ce in shiga falo ga shi nan zuwa. Na shiga ba a jima ba ya fito, muka gaisa ya ce, a wannan karo yana so ne mu tattauna kan abin da ya shafi kasa, ya kawo misali da abin da yake faruwa na rikicin manoma da Fulani makiyaya musamman a jihohin Taraba da Benuwai, ya ce wannan rikici yana daga masa hankali, kuma yana ganin an sanya Shugaban kasa Buhari a cikin tsaka-mai wuya. Ya ce yayin da al’ummar Fulani suke kallonsa a matsayin dansu da ya bari ake ta hallaka su, a gefe guda kuma sauran kabilu manoma suna kallon shi yake daure wa’ yan uwansa Fulani gindi suke hallaka su.

Malam Ali Wakili mutum ne mai saukin kai da tawali’u da mutunta dan Adam. Bai daukar kansa wani gingimemen mutum da huldarsa da sauran jama’a za ta zamo tamkar ta manyan dawa da sauran kananan dabbobi. 

Lokacin da za mu tattauna a wannan ranar ya sake nuna irin wannan saukin kai, inda ya nace cewa lallai sai in dawo kan kujerar da yake zaune mu zauna tare, duk da cewa kujerar da nake zaune a kusa da tasa take. Mun tattauna inda ya yi bayani mai tsawo kuma ya bukaci Shugaba Buhari ya cire Fulako ya fuskanci wannan batu gadan-gadan don a magance shi kowa ya huta.

Bayan mun tattauna matsalar manoma da Fulani makiyaya ne sai na bijiro masa da babbar matsalar da take ci wa jihata kuma jihar da yake wakilta tuwo a kwarya wato Jihar Bauchi. 

Wani abu da yake burge ni da marigayi Sanata Ali Wakili shi ne duk da cewa akwai takaddama a tsakaninsa da Gwamna Mohammed Abubakar na Jihar Bauchi, idan ka zauna da shi, ba ka isa ka zagi Gwamnan ko ka bata shi a gabansa ba. Yakan ce takaddamarsu ce ta manya kuma suna yi ne domin ganin an cika alkawuran da suka yi wa jama’ar Jihar Bauchi lokacin yakin neman zabe ba wai suna gaba da juna ba ne.

Tambayar da na yi masa kan wannan batu ita ce ta karshe a tattaunawar tamu, inda na tabo batun yunkurin sulhunta su da aka samu a baya-bayan nan. Ina samun labarin rasuwarsa sai na tuno irin bayanin da ya yi wanda nake kallo tamkar wasiyya ce ga duk wani dan siyasa da ya fito daga Jihar Bauchi da kuma kasar nan. A lokacin da aka buga hirar a Aminiya ta ranar 26 ga Janairu, 2018, ba a buga amsar tambayar har karshe ba, saboda karancin fili, don haka na kawo cikakkiyarta don tunawa da wannan jajirtacce kuma gwarzon Sanata mai kaifi daya wanda ya rayu yana gwagwarmaya kuma ya koma ga Allah yana gwagwarmaya don kyautata rayuwar jama’arsa ga abin da ya ce:

“Da ma ana fada ne? Ina ganin wani lokaci ku ’yan jarida da wadansu magoya baya da ba su san mene ne gaskiyar lamari ba, ku kuke azizitawa. Ana sulhu ne idan fada, alhali ba a dambarwa. Sai dai a ce an samu rashin fahimta, wanda kullum nake cewa a wurina ba an samu rashin fahimtar ba ne, don kyashi ko hassada (ko) don wani ya zama Gwamna ni ban zama ba. A’a magana ce ta cewa mu din nan in mun isa shugabanni, to abubuwan da muka ce za mu yi, mu yi kokari mu yi su. In muka ba mutane kalmar bakinmu, to mu tabbatar daga zuciyarmu ta fito. Allah Ya sani al’ummar Bauchi sun sani ina daya daga cikin masu ruwa-da-tsaki da ta sanadiyyarsu, Mai girma Mohammed Abubakar Allah Ya dora shi Gwamnan Jihar Bauchi, kuma yayin da muke tafiya ko ba a gan mu tare da shi ba, akwai alkawuran da muka dauka ga al’ummar jihar. Mun ce za mu yi zaben kananan hukumomi, mun kalubalanci gwamnatin da muka kayar ta Malam Isa (Yuguda) cewa ba ta yi zabe ba, muka ce za mu yi zabe cikin kankanen lokaci. Bayan haka, a wancan lokaci aka yayata wani abu da ya so kawo mana cikas cewa hakimai da dagatai da masu unguwanni sama da dubu uku (da aka kirkiro) in muka zo za mu rushe su. Allah Ya sani na rantse, Gwamna Abubakar ya rantse cewa mun fito daga manyan gidaje, muna da sarautun gargajiya in ba mu habaka wadannan sarautu ba, ba za mu tozarta su ba, amma sai aka wayi gari aka rusa su. Aka fake da cewa majalisa ta rusa su, majalisar nan fa, ba su fi 31 ba, 28 ’ya’yan Jam’iyyar APC ce, jam’iyyar da Gwamnan ya fito. Aka ce daya daga cikinsu da ya fito daga jam’iyyar adawa ya kawo shawarar rushe dokar da ta kirkiro masarautun, ta shige majalisa ta je gaban Gwamna ya sa hannu. Me za mu fada wa al’umma? Me za mu fada wa Allah? Ni ban dauki siyasa yaudara ba, saboda hakki ne za a tambaye ni a kai. Kuma mun yi alkawari ga shugabannin jam’iyya na kananan hukumomi 20, cewa kafin mu yi zaben kananan hukumomi su za a nada shugabannin riko na kananan hukumominsu, shugabannin mazabun unguwanni su zamo kansiloli. Allah Ya sa muka ci zaben nan da aka zo aka fara fatali da wannan.

Kuma mun ce dukiyar jihar da ke zuwa kowane wata za mu fada wa al’umma ga kudin da yake zuwa baitul-mali ga yadda aka yi da su, amma ba a yi haka ba, akwai shaida ta muryar Gwamnan kan haka.

Akwai abubuwan ci gaba da mutane suke tsammani, sai muka iske akwai tangarda kan biyan albashi da fansho, an saita na albashi, amma har yau ba a saita na fansho ko garatuti ba. Akwai abubuwa da dama da aka karya alkawari a kansu.

Ba gaba muke da Gwamna ba, so muke a gyara kura-kuran da ake yi. So muke mu cika alkawuran da muka yi ga jama’a lokacin da muke neman kuri’arsu. Ni da shi jam’iyyarmu daya ce, Jam’iyyyar APC, don haka ko yau aka cika wadannan alkawura shi ke nan bukatarmu ta biya. Kamar yadda na fada wa takwararku ta Ingilishi, Daily Trust, maganar ba ta ina yi masa katsalanda a kan yadda zai tafiyar da mulkinsa ba ne na Gwamna, huruminsa daban, hurumina daban. 

Na mance wata matsalar ita ce, lokacin da aka ci zabe mun ce duk wadanda suka sadaukar da kansu wajen kafa jam’iyyar nan da wadanda suka tsaya mata takara, tun daga matakan uguwanni ya kamata su zama masu ruwa-da-tsaki, muka ce duk wanda ya manna fosta wajen tallata jam’iyyar nan duk a dama da su matukar suna da akalla takardar sakandare kamar yadda tsarin mulki ya nuna. Amma ba wai muna tsoma masa baki ko ni Ali Wakili ina tsoma masa baki a mulkinsa ba ne.”

Allahu Akbar! A ranar Asabar 17 ga Maris din nan da misalin karfe 9:00 na safe ina gidanmu a Bauchi sai na buga masa waya don mu gaisa, na ce a raina wannan bawan Allah kusan kullum shi yake kira na, don haka bari in kira shi mu gaisa. Na kira wayarsa ta buga amma bai dauka ba, kuma saboda na san zai kira ni daga baya ban sake bugawa ba. Kwatsam, bayan na fita daga gida, sai wannan labari mai girgiza zukata ya riske ni cewa Malam Ali Wakili ya koma ga Ubangijinsa! Allah Ka jikan Malam Ali Wakili, Ka yafe kura-kuransa da gazawarsa, Ka sa Aljanna ce makomarsa, kuma Ka albarkaci zuriyar da ya bari.

Sai mun zo Malam Ali Wakili!