Da Dumi Dumi

Sanata Wamakko zai gina Jami’ar Kimiyya ta Arewa maso Yamma a Sakkwato

Sanata Wamakko
Sanata Wamakko

Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta bai wa Gidauniyar Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko damar kafa Jami’ar Kimiyya da Kere-Kere mai zaman kanta ta farko mai suna Jami’ar Kimiyya ta Arewa maso Yamma da za a gina a Sakkwato.

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi takardu guda goma na shirye-shiryen kafa jami’ar a hedkwatar Hukumar NUC da ke Abuja. Sarkin Yamman Sakkwaton ya bayyana cewa daukacin yankin Arewa maso Yamma babu jami’a mai zaman kanta da ke samar da guraben karatu ga dimbin daliban da ke neman shiga jami’o’i a fannin kimiya.

Sanata Aliyu Magatakarda ya bayyana cewa, Allah cikin ikonSa, Ya ba shi damar kammala kare aikinsa na digiri na uku a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya kara da cewa jami’arsa matasa sun bi sahun magabata ne wajen neman ilimi.

Sarkin Yamman, a jawabin da jami’in hulda da jama’arsa Bashir Rabe Mani, ya fitar ya bayyana cewa ya samar da ilimi kyauta a lokacin yana Gwamna a matakai daban-daban har tsawon wa’adin mulkinsa.

Da yake jawabi Shugaban Hukumar NUC, Farfesa Abubakar Rasheed, ya nuna damuwarsa kan rashin jami’a mai zaman kanta a Jihar Sakkwato.

ADVERTISEMENT

Daga nan sai ya yaba wa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kan tunanin kafa jami’ar domin ganin an daga martabar ilimi a yankin Arewa maso Yamma da kasa baki daya.

Share