✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanin Ubangiji da kulawarSa

Ya Ubangiji! Ka jarraba ni, Ka san ni. Ka sa duk abin da nake yi, Tun daga can nesa Ka gane duk tunanina. Kana ganina,…

Ya Ubangiji! Ka jarraba ni, Ka san ni. Ka sa duk abin da nake yi, Tun daga can nesa Ka gane duk tunanina. Kana ganina, ko ina aiki, ko ina hutawa, Ka san dukkan ayyukana. Tun kafin in yi magana Ka riga Ka san abin da zan fada. Kana kewaye da ni a kowane sashe, Ka kiyaye ni da ikonKa. Yadda Ka san ni ya fi karfin magana, Ya yi mini zurfi, ya fi karfin ganewata. Ina zan tafi in tsere wa ruhunKa? Ina zan gudu in tsere maKa? Idan na hau cikin samaniya Kana can, In na kwanta a Lahira kana can, in na tashi sama, na tafi, na wuce gabas, Ko kuma na zauna a can yamma da nisa, Kana can domin Ka bi da ni, Kana can domin Ka taimake ni. Da na iya rokon duhu ya ɓoye ni, Ko haske da yake kewaye da ni ya zama dare, amma har duhun ma, ba duhu ba ne a gare Ka, Dare kuwa haskensa kamar na rana ne. Duhu da haske, duk daya ne gare Ka.

Kai ne Ka halicci kowace gaba ta jikina, Kai ne Ka harhada ni a cikin mahaifiyata. Ina yabonKa gama Kai abin tsoro ne, Duk abin da Ka yi sabo ne, mai ban mamaki. Da zuciya daya na san haka ne. Ka ga lokacin da kasusuwana suke siffatuwa, Sa’ar da kuma ake harhada su a hankali A cikin mahaifiyata, Lokacin da nake girma a asirce. Ka gan ni kafin a haife ni. Ka kididdige kwanakin da Ka kaddara mini, Duk an rubuta su a littafinKa, Tun kafin faruwar kowanensu. Ya Allah! Tunani kanKa suna da wuyar ganewa a gare ni, Ba su da iyaka! In na ƙirga su, za su fi tsabar yashi, Sa’ar da na farka, har yanzu ina tare da Kai. Ya Allah! Da yadda nake so ne, da sai Ka karkashe mugaye! ’Yan ta-da-zaune tsaye kuma sai su rabu da ni! Suna ambaton mugayen abubuwa a kanKa, Suna fadar mugayen abubuwa gaba da sunanKa. Ya Ubangiji! Ga yadda nake ƙin wadanda suke kinKa, Da yadda nake raina waɗanda suke tayar maKa! Kiyayyar da nake yi musu ta kai intaha, Na dauke su, su abokan gabana ne. Jarraba ni, ya Allah! Ka san tunanina, Gwada ni, Ka gane damuwata. Ka bincike, ko akwai wani rashin gaskiya a gare ni, Ka bi da ni a madawwamiyar hanya.

Yabo domin alherinsa da ikonSa

Zan yi shelar girmanKa, ya Allahna, Sarkina, Zan yi maKa godiya har abada abadin. Kowace rana zan yi maKa godiya, Zan yabe Ka har abada abadin. Ubangiji Mai girma ne, dole ne a fifita yabonSa, GirmanSa ya fi karfin ganewa. Za a yabi abin da Ka aikata daga tsara zuwa tsara, Za su yi shelar manya-manyan ayyukanKa. Mutane za su yi magana a kan darajarKa da daukakarKa, Ni kuwa zan yi ta tunani a kan ayyukanKa masu ban mamaki. Mutane za su yi magana a kan manya- manyan ayyukanKa, Ni kuwa zan yi shelar girmanKa. Za su ba da labarin girmanKa duka, Su kuma rera waka a kan alherinKa. Ubangiji Mai ƙauna ne, Mai jinkai, Mai jinkirin fushi, Cike da madawwamiyar kauna. Shi Mai alheri ne ga kowa, Yana juyayin (tausayin) duk abin da Ya halitta. Ya Ubangiji! Talikanka duka za su yabe Ka, Jama’arKa kuma za su yi maKa godiya! Za su yi maganar darajar mulkinKa, Su ba da labarin ikonKa, Domin haka dukan mutane za su san manyan ayyukanKa, Da kuma darajar ɗaukakar mulkinKa. Mulkinka, madawwamin mulki ne, Sarki ne Kai har abada. Ubangiji Yakan taimaki dukkan waɗanda suke shan wahala, Yakan tada waɗanda aka wulakanta. Dukkan masu rai suna sa zuciya gare Shi, Yana ba su abinci a lokacin da suke bukata, Yana kuwa ba su isasshe, Yakan biya bukatunsu duka. Ubangiji Mai adalci ne a abin da Yake yi duka, Mai jinƙai ne a ayyukanSa duka. Yana kusa da dukkan waɗanda suke kira gare Shi, Waɗanda suke kiranSa da zuciya ɗaya. Yakan biya bukatar dukkan waɗanda suke tsoronSa, Yakan ji kukansu, Ya cece su. Yakan kiyaye dukkan waɗanda suke ƙaunarSa, Amma zai hallaka mugaye duka. A kullum zan yabi Ubangiji, Bari talikai duka su yabi sunanSa Mai tsarki har abada!

Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ka yabi Ubanigji, ya raina! Zan yabe Shi muddin raina. Zan rera waƙa ga Allahna dukkan kwanakina. Kada ka dogara ga shugabanni, Ko kowane mutum da ba zai iya cetonka ba. Sa’ar da suka mutu sai su koma turbaya, A wannan rana dukkan shirye-shiryensu sun kare. Mai farin ciki ne mutumin da Allah na Yakubu ne Yake taimakonsa, Yana kuma dogara ga Ubangiji Allahnsa, Wanda Ya halicci sama, da duniya, da teku, Da dukkan abin da ke cikinsu. Kullum Yakan cika alkawuranSa. A yanke shari’arsa Yakan ba wanda aka zalunta gaskiya. Yana ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji Yakan kuɓutar da ɗaurarru. Yakan ba makafi ganin gari. Yakan daukaka wadanda aka wulakanta. Yana kaunar jama’arSa, adalai. Yakan kiyaye baƙi waɗanda suke zaune a ƙasar. Yakan taimaki gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu. Yakan lalatar da dabarun mugaye. Ubangiji Sarki ne har abada! Ya Sihiyona, Allahnki zai yi mulki har dukkan zamunna! Yabo ya tabbata ga Ubangiji!

(Zabura 139,145,146)