✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanya hannun Buhari kan dokar Dokar Kudi: ’Yan Najeriya za su biya karin haraji mai yawa

‘Yan Najeriya za su fuskanci biyan karin kudaden haraji masu yawa, sannan farashin  wutar lantarki zai yi tashin gwauron zabo a dalilin sanya hannun da…

‘Yan Najeriya za su fuskanci biyan karin kudaden haraji masu yawa, sannan farashin  wutar lantarki zai yi tashin gwauron zabo a dalilin sanya hannun da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi a kan Dokar Kudi domin bunkasa hanyar samun kudin shiga ga Gwamnati.

A ranar litinin da ta gabatace Shugaban Kasar ya sa hannu a kan dokar, a fadarsa da ke  Abuja. Wannan yana zuwa ne wata biyu bayan da Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da kasafin kudin bana, ta kuma mika shi ga Shugaban domin rattaba hannu a cikin watan Nuwamban bara. Dokar ta amince da yin kari kan Harajin Kayayyaki (BAT) daga kashi biyar zuwa kashi bakwai da rabi cikin 100.

Aminiya ta gano cewa kasafin kudin bana  wanda ya kai Naira tiriliyan 10 da biliyan 590 (kimanin Dalar Amurka biliyan 35), ya dogara ne galibi a kan a sabon Harajin BAT.

Ra’ayin kwararru ya sha bamban a kan yadda za a aiwatar da sabon harajin; yayin da wasdanu ke ganin gwamnati za ta kara samun makudan kudi da zai jawo habakar tattalin arziki, wadansu suna ganin hakan zai kara jefa talakawa cikin mawuyacin hali.

Wata sanarwa da Kakakin Shugaban Kasa, Mista Femi Adesina, ya fitar a ranar Litinin da ta gabata ta ce, ana bukatar haraji mai yawa kafin a samu damar biyan kudaden kwangilar manyan ayyukan da gwamnati ke yi, musamman a bangaren lafiya da ilimi da kuma muhimman ayyukan raya kasa.

Tun farko Shugaba Buhari ya fitar da sanarwar sanya hannu da ya yi a kan sabuwar dokar ta shafinsa na ‘Twitter’ mai adereshin @MBuhari, inda  ya ce dokar ita ce za ta tallafa wa kasafin kudin bana.

Karin harajin dai zai shafi karuwar farashin kayayyaki da kari kan harajin kudin shiga na daidaikun jama’a da kamfanoni da kuma harajin kan hanya ‘tollgate.’

Sabuwar dokar za ta bukaci dukkan masu sayen kayayyaki  su nuna shaidar lambar biyan haraji (TIN) kafin su gudanar da wata huldar kudi a bankuna.

Sabuwar dokar ta yi wasu sauye-sauye ga harajin fetur da na Hukumar Kwastam da Hukumar Aikewa da Sakonni da kuma kudin fiton kaya da Harajin BAT da harajin ribar da aka samu a kan jari.

Farashin wutar lantarki zai yi sama sosai a watannin farko na 2020

Da aka tuntubi masana tattalin arziki game da karin harajin kayayyaki sun ce zai jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali sakamakon yadda farashin kayayyaki zai yi tashin gwauron zabo.

Dangane da karin farashin wutar lantarki kuwa, sabon farashin wutar zai fara ne a watan Afrilun bana, inda Hukumar Kula da Harkokin Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) da kamfanonin rarraba wutar lantarki (Discos) suka sanar da cewa za a fara biyan sabon farashin wutar lantarki a farkon bana. Wata kididdiga da aka fitar ta nuna cewa maitsakacin karin kudin wutar zai fara ne daga Naira 15 zuwa Naira 20 ga kowane kamfanin rarraba wutar lantarki.

Ganin yadda karin farashin wutar ke jawo fargaba, wata majiya da ke da alaka da masu lura da yadda farashin zai kasance ta shaida wa wakilanmu cewa, Hukumar NERC za ta fara karin farashin ne daki-daki. Kara farashin zai fara ne daga farkon watan Afrilun bana.

A wata tattaunawa da ya yi da Aminiya Ministan Makamashi Injiniya Sale Mamman, ya ce bangaren rarraba wutar lantarki a yanzu yana cin gashin kansane, don haka bangaren yana bukatar farashin da zai dace da yadda yake sanya wutar.

Karin harajin sadarwa yana nan tafe a Najeriya

Wakilan Aminiya sun ruwaito cewa Majalisar Kasa tana shirin kakaba harajin kashi  9 a bangaren sadarwa. Harajin na bangaren sadarwa zai shafi bangaren aikewa da tes da sako mai dauke da hotuna (MMS) da data gama su amfani da Intanet da masu kallon tashoshin talabijin.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana kudirinta na dawowa da harajin kan hanya wato ‘tollgate’ a fadin Najeriya, sai dai kwararru sun yi amanna cewa hakan zai jawo karin farashin kudin mota a kasar nan.

Ra’ayin kwararru a kan sabon karin haraji

Masu fashin baki sun yi karin haske kan sabuwar dokar haraji a ranar Litinin da ta gabata, sun ce karin zai dadada wa gwamnati wajen samun kudaden shiga. Sannan sun ce karin harajin zai yi illa ga ’yan Najeriya inda zai kassara samun ’yan kasa musamman idan karbar harajin ba a bi shi ta hanyar da ta dace ba.

A lokacin da take ganawa da Aminiya Farfesa Sarah Anyanwu, ta Sashen Tattalin Arziki da Ci gaba da ke Jami’ar Abuja, ta ce karin babu abin da zai haifar sai dai ya jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali. Ta ce karin harajin ya zarta sabon karin albashi da aka yi na Naira dubu 30 mafi karanci. Farfesar wacce ita ce Shugabar Kungiyar Tattalin Arziki ta Kasa (NES), ta ce ’yan Najeriya suna shakku kan ko za a bi hanyar da ta dace wajen kashe kudaden harajin da za a tara.

Wani kwararre mai kula da bangaren bincike na Kungiyar Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) Farfesa Ken Ife, a wata tattaunawa da aka yi da shi ta tarho ya ce “Mu ne muke da haraji mafi karanci a fadin Afirka inda ake karbar kashi 5 cikin 100, wanda kashi 15 cikin 100 shi ne harajin da ake karba a mafi yawan kasashen Afirka inda Ghana ce kasar da ta fi kowace yawan haraji inda take karbar kashi 17 cikin 100.”

Sai dai Farfesan ya bayyana damuwarsa inda ya ce harajin zai fi shafar masu sayen kayayyaki, ya ce “Abin damuwar a nan shi ne mu tabbatar mun kare talakawa daga shiga cikin mawuyacin hali ta hanyar kaurace wa karin farashin kayan abinci da magunguna, saboda kada mu tagayyara talakawa da suke zaune a garuruwanmu. Wannan shi ne dalilin da ya sa nake ba gwamnati shawara a kan ta cire Harajin BAT daga cikin  karin harajin da za ta yi,” inji shi.

Kungiyar Masu Samar da Ayyukan yi ta Kasa  (NECA) ta gargadi Gwamnatin Tarayya kan karin haraji

Kungiyar  NECA a nata bangaren ta ce tabbas Shugaban Kasa yana nufin alheri ne ga kasa, amma tana gargadin gwamnati wajen daukar matakan da suka dace.

Daraktan Kungiyar Dokta Timothy Olawale, ya ce kada gwamnati ta yi wa bangarori masu zaman kansu kallon “saniyar tatsa” a kokarin da take yi wajen tara kudaden shiga, babu abin da kudirin zai yi sai sake jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali kan wanda suke ciki tuntuni, sannan zai sake jefa ’yan kasa cikin matsanancin talauci maimakon a tsamo su daga halin da suke ciki.