Da Dumi Dumi

Sarauniyar kyau ta bana ta bayyana

Sabuwar kyau ta bana, EzineeA yayin da al’ummar Musulmi suka fara azumin Ramadana na bana cikin damina, shi kuwa otel din Intercontinental da ke bictoria Island Legas, tare da hadin gwiwar jihohin Edo da Ekiti da wasu kamfanoni, sun dauki nauyin shirya gasar sarauniyar kyau ne.
A bana, wacce ta lashe gasar, ita ce Mis Ezinee Akudo, ’yar shekara 22, wacce kuma ta kammala karatunta na Lauya a Jami’ar Jihar Abiya.
Sabuwar sarauniyar, ta doke abokan takararta ne su 20, inda har ma ta lashe gasar mai dacewa da hoto.
Kamar yadda sarauniyar ta ce: “Na yi matukar murna da lashe gasar nan. Akwai kyawawan mata da suka fafata a gasar nan, amma dai ni ce na lashe. Na gode wa Allah da wannan nasara.”
Wacce ta dora mata hular sarauta, ita ce tsohuwar sarauniyar kyau ta Najeriya, Grace Oyelude. Kadan daga kyaututtukan da suka hada da Naira miliyan uku da sabuwar mota, kirar Toyota Corolla da muhallin gida na tsawon shekara daya, da kuma daukar nauyin tafiya zuwa birnin California da ke Amurka. Haka kuma kamar yadda kamfanin MUD Cosmetics ya yi mata alkawari, za ta rika tafita duk garin da kake so a jirgi, a duk fadin Najeriya a aljihunsa.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya