Da Dumi Dumi

Sarkin Barebari a Legas ya kwanta dama

Marigayi sarkin Barebarin Munshi, a Legas, Mai Saleh Mustafa

Allah Ya yi wa Sarkin Barebarin  Munshin da ke jihar Legas, Mai Saleh Mustafa, rasuwa bayan ya yi fama da jinya ta karamin lokaci a gidan sa da ke yankin Matta a Ikorodu.

Sakataren Majalisar Sarkin Barebarin, Ahmad Tijjani Sulaiman, ya fitar da sanarwar rasuwar.

Ya ce za a yi jana’izar sa da safiyar Litinin, 18 ga watan Mayu, a Legas.

Kafin rasuwarsa, marigayi Mai Saleh, uba ne ga Kungiyar ‘Yan Arewa Mazauna Legas, kana daya daga cikin shugabannin Barebari a jihar Legas.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya