✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Fulanin Nasarawa ya bata da dansa kan siyasa

Sarkin Fulanin Nasarawa kuma Sakataren Kwamitin Dattawan Jam’iyyar PDP (BOT)  na kasa, Sanatab Walid Jibrin ya bata da dansa saboda dan yya shiga Jam’iyyar CPC.Wata…

Sanata Walid JibrinSarkin Fulanin Nasarawa kuma Sakataren Kwamitin Dattawan Jam’iyyar PDP (BOT)  na kasa, Sanatab Walid Jibrin ya bata da dansa saboda dan yya shiga Jam’iyyar CPC.
Wata takarda dauke da sanya hannun Sanata Walid Jibrin da ta mayar da martani kan labarin da jaridar Leadership ta ranar Litinin ta buga mai kanu: “dan Sakataren Dattawan PDP ya shiga CPC,” wadda aka buga a jaridar Daily Trust ta ranar Talata ta ce, Imrana dan marigayi (Guruf Kyaftin) Usman Jibrin dan uwan Sanata Walid Jibrin ne, don haka ba ya da iko da shi, amma yana iko da ’ya’yansa na cikinsa su goma.
Sanata Walid Jibrin wanda ya lissafo daukacin zuriyarsu mai dauke da ’ya’ya 51, ya zargi dan Usman Jibrin da ba da kansa araha wasu shugabannin CPC a Jihar Nasarawa su yi amfani da shi wajen bata masa sunan da ya wahala yana ginawa da zubar masa da mutunci da martaba.
Sarkin Fulanin ya ce laifinsa a wurin abokan adawa shi ne PDP c eke juya akalar siyasar mazabarsa da karamar hukumarsa kuma ita ta mamae jihar. “Kuma suna adawa da biyayyattta ga Shugaba Goodluck Jonathan da Mataimakinsa Namadi Sambo,” inji shi.
Sanata Wali Jibrin wanda ya ce shigar Imrana dan Usman Jibrin cikin harkokin siyasa zai karfafa imaninsa ne da goyon bayan da yake ba PDP a Jihar Nasarawa da Najeriya, ya nemi magoya bayan PDP a Jihar Nasarawa da mazabarsa ta Laminga su kwantar da hankalinsu domin babu wata baraka a iyalan Jibrin.
Ya ce, zai ci gaba da girmama dan uwansa Usman Jibrin da matansa hudu da sauran ’ya’yansa “Kuma rashin biyayya da ladabin Imrana ba zai canja halina kan iyalan Usman Jibrin ba. Dangantaka za ta ci gaba da kara karfafa da su duka,” inji sanarwar.