Da Dumi Dumi

Sarkin Guragun Jihar Filato ya yaba wa Gwamna Lalong

Malam Idris Abdullahi Sarkin Guragun Filato
Malam Idris Abdullahi Sarkin Guragun Filato

Sarkin Guragun Jihar Filato Malam Idris Abdullahi ya yaba wa Gwamnan Jihar, Barista Simon Lalong kan yadda yake tafiya da al’ummar Musulmin jihar a gwamnatinsa, sabanin gwamnatocin da suka gabata.

Sarkin Guragun  ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya a garin Jos.

Ya ce tunda Gwamna Lalong ya hau kujerar Gwamnan Jihar Filato yake tafiya da al’ummar Musulmin jihar cikin mutunci a gwamnatinsa, tare da nada Musulmi a muqamai daban-daban da kuma tallafa wa al’ummar Musulmin a kowane lokaci.

Ya ce ko a aikin Hajjin bana Gwamna Lalong ya dauki nauyin biyan kudin kujerun aikin Hajji 630, aka raba wa al’ummar Musulmin jihar kyauta.

“Hatta mu naqasassu mun amfana da wadannan kujerun aikin Hajji da Gwamna Lalong ya bayar. A duk Najeriya babu Gwamnan da ya bayar da kujerun aikin Hajji kamar yadda Gwamnan Lalong ya yi,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Sai ya yaba wa Gwamnan kan jajircewar da yake yi wajen ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Filato.

Ya ce don haka kullum suke yi masa addu’ar fatar alheri kan wannan qoqari da yake yi.

Ya yi kira ga Gwamna Lalong ya ci gaba da kulawa da naqasassu musamman a bangaren zuwa aikin Hajji domin su riqa zuwa suna roqon Allah Ya kawo zaman lafiya a Jihar Filato da Najeriya baki daya.

Sannan ya yi kira ga al’ummar Musulmin Jihar Filato su ci gaba da bai wa Gwamna Lalong goyon baya da hadin kai, domin ya ci gaba da samun nasarori kan qudirorin da ya sanya a gaba na ciyar da jihar gaba.

Share