✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Hausawa zai yi wa Hakimansa garanbawul

A makon jiya ne mai martaba Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji Ahmad Zungeru ya sha alwashin yi wa Hakimansa garanbawul biyo bayan koken da jama’ar garin…

A makon jiya ne mai martaba Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji Ahmad Zungeru ya sha alwashin yi wa Hakimansa garanbawul biyo bayan koken da jama’ar garin Sabo-Ibadan suka yi na rashin tabuka abin a zo a gani da suke zargin hakiman su 80 da shi.

Al’ummar garin Sabo Ibadan sun yi koken ne a sa’ilin taron ci gaban al’umma da kungiyar garin Nagarke ta shirya wa al’ummar Arewa mazauna garin Sabo Ibadan taron da ya sami halartar ‘yan asalin yankin daga sassa daban daban na kasar nan wadanda suka tattauna al’amura da dama da suke damun al’umar yankin ciki harda matsalar nan ta shaye-shaye a tsakanin matasa da mata da saye da sayar da kayan sata, da koma baya ta fuskar ilimi da siyasa lamarin da suka alakanta shi da rashin tsarin shugabanci nagari, da rashin hada kai da taimakon juna

A jawabin da Sarkin Hausawan Ibadan, ya gabatar a taron, Dakta Ahmadu Zungeru ya shaida cewa kaso mafi yawa a cikin Hakiman fadarsa basu san junan su ba, domin basa shirya tarukan ci gaban jama’ar su, ya ce wannan na cikin abubuwan da ke janyo koma baya tsakanin Hausawa a garin Ibadan.

A tattaunawar da Aminiya tayi da Sarkin Hausawan jim kadan da kammala taron inda ya shaida cewa, an kafa kwamitin mutum 10 da za suyi aikin tantance Hakiman nasa, “Kasan wannan tsari ne na sarautar gargajiya ba na gwamnati ba, idan ‘yan kwamitin sun kammala aikin su zasu kafe sunaye duk Hakimin da bai ga sunan sa ba an kore shi ke nan, sai dai amma ya iya nema a nan gaba idan ya gyara za kuma mu surka da matasa, kuma duk Hakimin da aka kora koda ya sake nema sai ya yi alkawarin zai tsaya bil hakki da gaskiya ya yi aiki tare da jama’a, zai taimakawa garin nan, sannan zai taimakawa mutane.” in ji Sarkin Hausawan Ibadan.

Sarkin Hausawan, ya nuna farin cikin shi da taron da kungiyar Nagarke ta shirya ya ce, sun farfado da tarihi mai kyau wanda kakannin su suka kafa a baya, “Wannan tsari ne mai kyau da wasu matasa da dattawanmu suka farfado da shi, nayi murna kwarai da wannan na kuma yi mamaki ta yadda aka dawo da wannan kyakkyawar akida ta ci gaba, ta taimakawa juna tare da basu shawarar wannan abu ne da kakannin mu suka asassa a baya tun daga kan marigayi Nagarke, wanda da an manta da shi amma iyaye sun tabo shi kadan bayan sun kau an yi watsi da shi nayi mamaki da Allah ya taso da wasu matasa har ma da dattawa wadanda suka ga ya dace a dawo da wannan kyakkyawar akida ta ci gaba dan haka ina kira ga jama’a da su basu goyon baya ina kuma fatan Allah Ya dafa masu.” In ji shi.

Alhaji Abdullahi Lawal Marafan Ibadan, daya ne daga cikin dattawan da suka yi tsokaci a sa’ilin taron kana daya ne daga cikin Hakimai 80 na garin Ibadan a jawabin da ya yi a sa’ilin taron ya musanta maganar cewa, rashin tabuka abun azo a gani na Hakimai ne ya janyo tabarbarewar al’amura, “ Ni ina ja da wannan maganar, ban yarda da ita ba, domin sallah daga liman ta ke baci, idan sama tayi kyau akwai tabbacin kasan ma zata yi kyau, dan haka kamata ya yi mu fadawa kawunan mu gaskiya, iyaye su kula da tarbiyyar ‘ya’yansu, su baiwa ilimi mahimmanci domin ilimi shi ne ginshikin rayuwa.” In ji shi.

Ya kuma yi alkawarin daukar nauyin karatun gaba da sakandare na yara 10 a ‘yan garin Sabo ibadan a wannan shekarar ya ce, ya yi haka ne domin bada gudunmawarsa na tarbiyyar al’umma.

A zantawar da Aminiya tayi da Marafan na Ibadan ya shaida cewa, shekara mai zuwa ma in Allah Ya yi masa tsawon rai zai sake daukar nauyin yara 10, 5 wadanda suka ci jarabawar WAEC, 5 wadanda basu ci ba, ya ce zai kuma sa a koya masu sana’a, “ zan ci gaba da yin wannan har tsawon raina, ina fatan wasu ma su yi koyi ta haka zamu taimaki al’ummar mu, domin ilimi da abin dogaro su ne mafita,’ inji shi.

Kungiyar Garin Nagarke ce, ta shirya taron domin lalubo bakin zaren ci gaban al’umar Hausawan Sabo Ibadan an kuma bai wa jama’a da dama damar tofa albarkacin bakin su ciki har da iyaye mata kana taron ya karkata ne bisa al’amuran da ke ciwa al’umar garin Sabo Ibadan tuwo a kwarya.