✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Hausawan Jihar Kwara ya yi gangamin taron sarakuna

Watanni biyu bayan nada sabon Sarkin Hausawa na Jihar Kwara, Alhaji Abubakar Ibrahim, Maji-Dadin Sarkin Gobir, ya fito da sabon salon mulkin jama’arsa ta hanyar…

Watanni biyu bayan nada sabon Sarkin Hausawa na Jihar Kwara, Alhaji Abubakar Ibrahim, Maji-Dadin Sarkin Gobir, ya fito da sabon salon mulkin jama’arsa ta hanyar gayyatar sarakunan Hausawa na garuruwa daban-daban domin tattaunawa kan samo hanyar magance matsalolin rayuwa da suka dabaibaye al’ummar Hausawa a jihar.
Sarki Abubakar Ibrahim, ya kira taron farko a ranar Lahadi da ta wuce, inda aka tattauna al’amura daban-daban da suka shafi ci gaban jama’arsu.
Cikin sanarwar bayan taro da babban sakataren  sarki, Alhaji Yusuf Abdullahi Shiga ya karanta wa ’yan jarida a fadar sarkin da ke Zango, cikin birnin Ilori, ya ce, “mihimmin abu na farko da Sarki Abubakar Ibrahim, ya fi mayar da hankali kansa shi ne, shawartar dukkan sarakunan Hausawa na jihar su dukufa wajen lura da batun tsaro, su rika kusantar jami’an tsaro na yankinsu tare da hanzarta ba su labarin bullar abubuwan da ba su amince da su ba. Da kuma kula da dangantakarsu da mutanen da suke zaune tare da su da baki masu yawon ci-rani da girmama dokokin mahukunta.
Ya ce taron ya amince za a rika gudanar da shi a ranar Lahadin karshen kowane wata, inda kowane sarki zai kawo sakamakon abubuwan da suka faru a yankinsa da irin koke-kokensa da shawarwarinsa kan hanyoyin samun cigaba.
Sakatare Yusuf ya ce sabon salon yin taron a kowane wata ne zai samar da hanyar kafa majalisar sarkin Hausawan jihar ta Kwara, wacce alhakin tafiyar da al’amura da suka shafi al’ummar Hausawa a jihar ya rataya a wuyanta.
Da yake zantawa da wakilinmu jim kadan bayan kammala taron, Sarkin Hausawan Offa, Alhaji Usman Isma’ila ya ce, “dukkanmu mun yi na’am da irin shawarwarin da Sarkin Abubakar Ibrahim ya ba mu kuma har mun fara aiwatar da wasu shawarwarin domin cigaban mutanenmu da Jihar Kwara baki daya. Wannan shi ne karo na farko da muka samu jagora mai fafutukar ganin mun kusanci mahukunta domin samo hanyar cigabanmu. Ya kamata mu ba shi hadin kai da goyon baya tare da yi masa addu’ar rokon Allah (TWT) Ya yi masa jagoranci. Ina kira ga sauran jama’a su zo mu tafi tare domin tsira tare.”