✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Ilori ya yi wa Buhari godiyar nadin Gambari

Mai Martaba Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari, ya yi godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari saboda nadin Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar…

Mai Martaba Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari, ya yi godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari saboda nadin Farfesa Ibrahim Gambari a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.

A wata sanarwa da mai ba shi shawara a kan harkokin yada labarai, Mallam Abdulazeez Arowona, ya sanyawa hannu, Sarkin ya ce nadin wata karramawa ce gagaruma ga daukacin al’ummar Masarautar Ilori.

Sai dai kuma har yanzu Fadar Shugaban Kasar ba ta tabbatar da nadin Farfesa Gambari ba.

Mashawartan shugaban kasar a kan al’amuran yada labarai da ma jami’an ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya sun ki su ce uffan a kan lamarin.

Sai dai sun bukaci manema labaran da suka tuntube su da su jira sanarwa a hukumance.

Idan nadin ya tabbata dai, Farfesa Gambri ne zai gaje kujerar marigayi Abba Kyari wanda ya riga mu gidan gaskiya a watan jiya bayan ya yi fama da wata larurar da COVID-19 ta ta’azzara.