✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Kano ya bukaci a samar da hukumar da ke kula da masu wa’azi

An bayyana rashin bibiya da kula da masu wa’azi game da irin wa’azin da suke gudanarwa a matsayin abin da yake basu damar fito da…

An bayyana rashin bibiya da kula da masu wa’azi game da irin wa’azin da suke gudanarwa a matsayin abin da yake basu damar fito da akidun da suke kawo rigingimu tare da tayar da kayar baya a kasar nan.

Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhamamdu Sanusi II ne ya bayyana haka a lokacin taron kasa na kwana uku akan taryar da kayar bayan ‘y’ayan kungiyar Boko Haram a Najeriya wanda Cibiyar Addinin Musulunci da Tattunawa Tsakanin Mabanbantan addinai ta Jami’ar Bayero tare da hadin kan ofishin  kasa da ke Najeriya suka shirya.

Sarkin Kanon ya nemi gwamnati  ta samar da wata hukuma da za ta rika kula da masu yin wa’azi a wuraren ibada don gano masu muggan akidu tare da dauakr matakin tun kafin su kai ga yin barna.

Har ila yau Sarkin Kano ya bayyana takaicinsa game da yadda a kasar nan ke jingine masu ilimin addini a gefe tare da yi musu kallon jahilai, inda ya yi kira ga gwamnati da ta samar da yanayin da zai bayar da dama ga irin wadanda suke da wancan ilimi su sami kulawa a gwamnati ta hanyar kallonsu a masu ilimi.

“wai a kasar nan duk ilimin da mutum yake da shi indai bai iya turanci ba to kallon jahili ake yi masa, wannan ba daidai ba ne.  Hakan shi yake kawo masu wancan ilimi su rika jin zafin an jingine su a gefe, kai kana zagin nasu ilimin su ma suna zagin naka”

Shi ma a jawabinsa tunda farko Shugaban Cibiyar CICID da ke Jami’ar Bayero, Dokat Bashir Aliyu Umar ya bayyana cewa sun shirya taron ne domin a samar da tarihin wannan rikici na Boko Haram domin a fahimci gaba dayan lamarin don amfanin na baya.

“Wannan taro zai bayar da damar tatatuanwa game da wannan rikici na Boko Haram tun daga samuwarsa da irin akidun mambobin kungiyar da sauransu, haka kuma za a ga irin matakan da gwamnati ta dauka akan lamarin. Taron kuma zai bayar da shawarwari wadanda za su taimaka wajen gano hanyoyin da za a yi maganin irin wannan fitina anan gaba da kuma lalubo hanyoyin yadda za a inganta rayuwar wadanda wannan fitina ta shafa kai tsaye,” inji shi.

A takardar da ya gabatar bako mai jawabi Farfesa Mukhtar Umar Bunza daga Jami’ar Usmanu Danfodiyo ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara mayar da hankali ga bangaren  makomar wadanda rikicin Boko Haram ya shafa ta hanyar sake gina musu mazaunnsu na dindindin da samar musu da ayyukan yi.