Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Sarkin Kano ya ce a bar Hukumar INEC ta yi aikinta

Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya nemi al’ummar Jihar Kano su zauna lafiya tare da kyale Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta  ta Kasa (INEC) ta yi aikinta yadda ya dace.

Sarkin ya yi wanan kira ne bayan Hukumar INEC ta ce zaben jihar bai kammala ba, lamarin da ya jefa al’ummar jihar a cikin rudani.

ADVERTISEMENT

Yayin da yake jawabi ga manema labarai, Sarkin ya tunatar da jama’ar jihar game da matsayin Hukumar INEC kan zaben Gwamnan Jihar inda ya ce akwai dalilan da suka sa hukumar ta dauki wannan mataki, “Muna tunatar da al’umma cewa Hukumar INEC ta ce zabe bai kammala ba saboda yadda aka soke zabe a wasu wurare. Kuma kada jama’a su manta INEC ta riga ta bayyana yawan kuri’un da kowane dan takara ya samu. Wadanan kuri’u suna nan a lissafe babu dan takarar da aka hana shi kuri’unsa a yanzu kuma da za a sake zabe a wasu wurare, inda za a hada da abin da kowane dan takara zai samu akan abin da ya riga ya samu tunda farko, don haka babu wani abu da yake a boye da zai kawo tashe-tashen hankula,” inji Sarkin.

Sarkin ya kara da cewa, “Ina kira ga al’ummar Jihar Kano su tuna cewa jiharmu tana da martaba kuma duk duniya ana kallon abin da ke faruwa, don haka mu guji duk abin da zai janyo wa jihar zubewar mutuncinta a wurin jama’a. Siyasa ba yaki ba ce duk wanda mutane suka zaba a ba shi, wanda kuma bai samu ba ya hakura ya karbi kaddara. Idan Allah Ya kai mu wani lokacin bayan shekara hudu sai ya nema. Wannan shi ne dadin dimokuradiyya.”

ADVERTISEMENT

Sarkin ya yi kira ga al’umma su kauce wa jita-jita domin a cewarsa jita-jita na haifar da rigima a cikin al’umma.

Sarkin ya kuma jinjina wa Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano Muhammad Wakili bisa jajircewarsa, “Mutanen Kano suna murna da canjin da ya kawo a Rundunar ’Yan sanda. Babu shakka ya dawo da martaba da kimar aikin ’yan sanda da kuma yarda da mutane ke da ita a kan ’yan sanda. Muna addu’ar Allah Ya sa ya dore a kan abin da ya faro domin ya ci gaba da samun yardar jama’ar jihar,” inji Sarkin.