✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Kano ya goyi bayan rufe iyakokin Najeriya

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na biyu ya bayyana amincewarsa game da rufe iyakokin kasashen da ke mokobtaka da Najeriya.inda ya ce, hakan ne kawai mafita…

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na biyu ya bayyana amincewarsa game da rufe iyakokin kasashen da ke mokobtaka da Najeriya.inda ya ce, hakan ne kawai mafita wajen magance fasakwaurin da ake yi ta hanyoyin iyakar kasar.

Sarkin, yaba wa Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari kan matakin rufe iyakokin kasar daga shigar da abubuwan da ake iya samarwa a cikinta.

Sarkin na Kano, ya kara da cewa Najeriya ta dauki matakin rufe dukkan iyakokinta ne, domin ta bunkasa tattalin arzikinta musamman abin da ya jibanci noma.