Da Dumi Dumi

Sarkin Karaye ya  rusa majalisarsa

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje

Sarkin Karaye da ke Jihar Kano Dokta Ibrahim  Abubakar II ya sauke wadansu daga cikin masu rike da sauratun gargajiya da ke masarautarsa.

Bayanin sauke su yana dauke ne a wata takardar da ta fito daga Karamar Hukumar Karaye dauke da sa hannun Jami’in Hulda da Jama’a na Karamar Hukumar Malam Haruna Gunduwawa.

Aminiya ta samu bayanin cewa an bayar da sanarwar sauke masu rike da sarautun ne bayan da Sarkin ya gana da su a fadarsa a ranar Juma’ar da ta gabata.

Sai dai Magajin Garin Karaye Injiniya Shehu Ahmed ya ce saukewar ba ta shafi hakimai takwas da ke masarautar ba.

Sarkin ya ce masarautar a shirye take ta kara fadada  sarautun masaurautar inda ya bayar da tabbacin cewa wadansu daga cikin masu rike da sarautun za su dawo kan gadajensu yayin da za a daga darajar wadansunsu.

ADVERTISEMENT

Haka kuma Sarkin ya mika godiyarsa ga masu rike da sauratun gargaiyar bisa gudunmawarsu wajen ciyar da masarautar gaba.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya