✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Kazaure ya hori talakawa su ba da gudunmawa ga tsaron kasa

Mai martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussaini Adamu ya ja hankalin al’ummar masarautarsa kan su sanya ido kan mutanen da suke kaiwa da dawowa a…

Mai martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussaini Adamu ya ja hankalin al’ummar masarautarsa kan su sanya ido kan mutanen da suke kaiwa da dawowa a cikin al’umma.

Sarkin ya yi kiran ne a ranar Litinin da ta gabata a fadarsa lokacin da ya yi Hawan Bariki, inda ya hori jama’a su sanya ido a kan batagarin mutane da suke shigowa cikin al’umma su fake suna aikatar miyagun ayyuka domin ta yin haka ne za a iya maganin duk wata matsala da za ta cutar da jama’a.

Daga nan ya nemi manoma su kiyaye wajen fitar da zakka a lokacin da suka girbe amfanin gonarsu, sannan ya shawarci mutane su dage wajen yin addu’a da ibada kuma su rika kauce wa aikatar fasadi sannan su kula da ’ya’yansu wajen hana su aikata miyagun ayyuka domin hakan zai taimaka wajen kauce wa fushin Allah.

Sarkin ya kuma shawarci iyaye su dage wajen bai wa ’ya’yansu ilimin addini da na zamani kuma su tsaya tsayin-daka wajen kare hakkin iyalansu.

Sarkin ya yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan ayyukan raya kasa da tsaro da yake yi, sannan ya yaba wa kananan hukumomin yankin da gwamnatin jiha saboda gudunmawar da suke ba su wajen Hawan Sallah a duk shekara.