✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Lafiya ya bukaci ’yan jarida su rika yada alheri

Mai martaba Sarkin Lafiya Alhaji Sidi Bage ya bukaci ’yan jarida a kasa baki daya su rika gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da rikon amana.…

Mai martaba Sarkin Lafiya Alhaji Sidi Bage ya bukaci ’yan jarida a kasa baki daya su rika gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da rikon amana.

Sarkin ya yi kiran ne lokacin da Kungiyar ’Yan jarida ta Kasa reshen jihar ta kai masa ziyarar ban girma a fadarsa da ke Lafiya. Sarkin ya ce kiran ya zama wajibi idan aka yi la’akari da muhimmancin aikin jarida ga gwamnatoci a dukkan matakai da al’umma baki daya. Ya ce “Ba shakka ’yan jarida suna da matukar muhimmanci a idon duniya, kuma za su iya ginawa ko rusa kasa. Saboda haka ne ya sa nake rokonku ku kasance ’yan jarida nagari a lokacin da kuke gudanar da aikinku musamman nemo wa kasar nan mafita daga kalubalen da take fuskanta a yanzu don amfanin al’umma baki daya maimakon yada munanan ayyuka da za su jawo mana bakin jini a kasashen waje,” inji shi.

Ya yi alkawarin cewa Masarautar Lafiya da sauran masarautun jihar  za su ci gaba da bai wa ’yan jarida a jihar da kasa baki daya cikakken goyon baya don tabbatar da cimma burinsu na yada labaran jihar da kasa yadda ya dace.

Tun farko da yake bayyana makasudin ziyarar, Shugaban Kungiyar, Mista Isaac Opukju ya ce kungiyar ta ziyarci Sarkin ne don neman albarkarsa da goyon bayansa wajen gudanar da ayyukanta a jihar. Ya yaba wa Sarkin dangane da dimbin nasarorin da ya cimma cikin lokaci kalilan.