✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Musulimi ya bukaci a daina dora alhakin miyagun ayyuka ga wata kabila

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya ce bai dace a rika dora alhakin miyagun ayyuka da ake yi a Najeriya a kan wata…

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya ce bai dace a rika dora alhakin miyagun ayyuka da ake yi a Najeriya a kan wata kabila ko al’umma daya  ba domin kowace kabila tana da irin wadannan miyagun mutane a cikinta. Ya ce, jin dadin yayata wannan al’amari da wadansu ke yi ba zai zama mai amfani ga kowa ba.

Sarkin Musulmi ya fadi haka ne cikin wata lacca da ya gabatar a wajen taron bikin Ranar Ulefunta na Akure da aka yi a ranar Litinin da ta gabata. Ya ce, “Halaye ne na dan Adam ba halin wata kabila ba ce. Kuma za a iya yin maganin wasu daga cikin wadannan halaye da suke da nasaba da tattalin arziki idan aka samar da ayyukan yi ga jama’a.” Sarkin Musulmin wanda ya halarci taron wuni biyu da Cibiyar Tuntuba a Tsakanin Addinai (NIREC) ta shirya a garin Akure hedkwatar Jihar Ondo ya ce ’yan siyasa ne suke ruruta wutar rikicin addini da kabilanci a cikin kasa domin biyan bukatunsu.

Ya yi kira ga al’ummar Najeriya su dawo daga rakiyar irin wadannan ’yan siyasa da suke amfani da dukiyarsu wajen cakuda siyasa da addini domin cimma burinsu. Ya ce, manyan littattafan addinanmu biyu Alkur’ani da Baibul babu wanda aka danganta shi da wata jam’iyyar siyasa.

Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Rabaran John Ayo Oladapo da Shugaban Kungiyar Limamai da Malamai ta Kasa Alhaji Ahmed Aladesawe ne suka jagoranci zaman taron na wuni biyu da ya samu halartar manyan masana da malaman addinai da sarakuna. Bayan kammala taron ne Sarkin Musulmin ya kai ziyarar ban girma ga Gwamna Rotimi Akeredelu na Jihar Ondo a ofishinsa a Akure.