✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Musulmi ya bukaci a hukunta maharan Mambila da Numan

Mai Martaba Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar na uku ya bukaci gwamnatin tarayya ta kamo wadanda suka kashe mata da kananan yara a garin Mambila da…

Mai Martaba Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar na uku ya bukaci gwamnatin tarayya ta kamo wadanda suka kashe mata da kananan yara a garin Mambila da Numan.
Sarkin Musulmin ya yi kiran ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin bikin kaddamar da gidan rediyo na farko da zai rika yada shirye-shiryensa a harshen fillanci mai suna Rediyo Pulaaku wanda Lamidon Adamawa, Dokta Muhammad Barkindo Mustapha ya kafa.