✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Qatar ya amince da murabus din Firayi Ministan kasar ya nada sabo

Sarkin Qatar ya nada sabon Firayi Ministan kasar, karkashin wata doka kamar dai yadda kafafe yada labaran kasar suka sanar. Kamfaninn dillancin labaran kasar, ya…

Sarkin Qatar ya nada sabon Firayi Ministan kasar, karkashin wata doka kamar dai yadda kafafe yada labaran kasar suka sanar.

Kamfaninn dillancin labaran kasar, ya ruwaito a yau Talata cewa, Sarki Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya amince da murabus din Firayi Minista Sheikh Abdullah bin Nasser bin Khalifa Al Thani ya yi.

Sarkin ya sanar da sunan Sheikh Khalid bin Khalifa bin Abdulaziz Al Thani a matsayin sabon Firayi Minista kuma Ministan cikin gida na kasar da ke yankin tekun Pasha.

Sheikh Khalid, ya sha rantsuwar kama aiki ne a gaban Sarkin, a wani bukin da ya samu halartar Wazirin Sarkin, Sheikh Abdullah bin Hamad Al Thani.

Sabon Firayi Ministan, ya kasance shugaban ofishin Sarkin, mai suna ‘Amiri Diwan’, gabanin nadin nasa da aka yi yau.

Ya kuma yi aiki a ma’aikatar iskar gas, kuma ya yi karatu a Amurka kafin daga bisani ya fara aiki da Sheikh Tamim lokacin yana Yarima mai jiran gado.

Ta kafar sadarwar Tiwita, Sheikh Abdullah, ya gode wa Sarkin sakamakon yadda ya dora shi bisa tafarki na gari, a lokacin yana Firayi Minista.