Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Sarkin Saminaka ya nada Dagacin Kayarda

Alhaji Abdulhamid Muhammad, sabon Dagacin Kayarda

Sarkin Saminaka ya nada Dagacin Kayarda

Mai martaba Sarkin Saminaka da ke Jihar Kaduna, Alhaji Musa Muhammad Sani ya nada Alhaji Abdulhamid Muhammad a matsayin sabon Dagacin Kayarda. An nada sabon dagacin a fadar Sarkin da ke Saminaka a ranar Alhamis din makon jiya.

Sabon Dagacin, an nada shi ne bayan da aka yi shekara uku ana takaddama kan sarautar a tsakanin tsohon Hakimin Kayarda Alhaji Bello Zubairu da tsohon Dagacin garin Malam Ibrahim Zubairu kan wanda za a nada, kan wannan sarauta.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ba da umarnin a nada Alhaji Abdulhamid Muhammad, wanda da ne ga masu takaddamar.

Da yake jawabi a wajen nadin Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani, ya  ce an  nada sabon Dagacin ne, bayan da aka yi shekara uku ana takaddama a kai a tsakanin tsohon Hakimin garin da tsohon Dagacin garin kan wanda za a nada.

Ya yaba wa al’ummar garin   kan yadda suka kwantar da hankalinsu, suka yi hakuri kan wannan matsaya da gwamnati ta dauka, na nada sabon dagacin.

Ya yi kira ga sabon dagacin ya yi kokari ya rike al’ummar garin tsakani da Allah, domin ganin an ci gaba da samun zaman lafiya da ci gaba a garin.

Da yake zantawa da Aminiya bayan kammala nadin, sabon Dagacin Alhaji Abdulhamid Muhammad ya mika godiyarsa ga Gwamnatin Jihar Kaduna, kan kokarin da ta yi wajen warware wannan matsala.

Har ila yau ya mika  godiyarsa  ga tsohon Hakimin garin  da tsohon Dagacin  garin kan hakurin da suka yi, aka ba shi wannan sarauta.

“Ina kira kan su yafe wa junansu, su manta da abubuwan da suka faru a baya. Kuma ina tabbatar musu cewa ni mai bin dukkan shawarwarin da za su ba ni ne a wannan gari, kan wannan sarauta da aka nada ni  a matsayina na da gare su,’’ inji shi.

Haka kuma ya  yaba wa Sarkin Saminaka kan kokarin da ya yi wajen warware wannan matsala.

Daga nan ya mika godiyarsa  ga al’ummar garin kan yadda suka yi tururuwa zuwa wajen wannan nadi, kuma suka  amince aka nada shi a wannan sarauta.