✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarki Sanunsi ya nada Mista Mike Wakilin ’Yan Chinan Kano

Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi ll ya nada Mista Mike Zhong Wakilin Yan Chinan Kano. Mista Mike wanda a yanzu ya zama Wakilin…

Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi ll ya nada Mista Mike Zhong Wakilin Yan Chinan Kano.

Mista Mike wanda a yanzu ya zama Wakilin Yan Chanan Kano, hamsahkin Dankasuwa ne a jihar Kano da ya shafe shekara kimanin 17 yana cudanya irin ta kasuwanci da ’yan kasuwa daban-daban a Jihar Kano.

Da ya ke bayaninsa jim kadan bayan kamala nada Mista Mike a matsayin Wakilin Yan Chanan Kano Sarki ya ce, “Mun nada ka Wakilin Yan Chinan Kano ne sakamakon irin gudummawar da kake bayarwa ta fuskar habaka kasuwanci da tattatalin arzikin Jihar Kano da ma Najeriya baki daya. Irin wanan gudummawa da kake bayarwa ka cancanci irin wannan karramawa daga Masarautar Kano domin hakan zai kara dankon zumunci a tsakanin al’ummar Kanawa da Yan Chana.

“Ina horonka da ka ci gaba da irin wannan kyakkyawan hali naka domin ci gaban al’ummar kasarnan da kuma Yan kasarka ta chana. Mu na sane da irin kokarin da kake yi na wanzar da zaman lafiya da karkafa harkokin cinikayya tsakanin Kanawa da jama’arka ta chana. Masarautar Kano na fatan ganin ka ci gaba da bunkasa harkokin kasuwanci a yankinta kamar yadda ka ke yi a yanzu.”

Shi ma da yake tattaunawa da Aminiya jim kadan kafin nada Mista Mike a matsayin Wakilin Yan Chanan Kano, Dan Malikin Kano, Ambasada Ahmad Umar ya jaddada cewa ba bu shakkan nadin na Mista Mike zai kawo ci gaban harkokin kasuwanci a tsakanin Al’ummar Jihar Kano da ta yan chana.

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, Mista Roby wanda shi ma mutumin China ne kuma managa ne a daya daga cikin Kamfanonin Mista Mike, ya bayyana farincikinsa da wannan nadin sarauta da aka yi wa Dan uwansa kuma maigidansa.

“Hakika a yau ina cike da farin ciki sosai sakamakon nada Dan uwana da Masarautar Kano ta yi a matsayin Wakilin Yan Chanan Kano. In takaice maka dai ji nake yi kamar an mayar da ni Da na halali a Jihar Kano. Wannan al’amari ba karami ba ne a wurin mu al’ummar Kasar Chana domin kuwa an karrama mu matuka kuma mung ode sosai.

“Ina mai tabbatarwa Masarautar Kano da ma al’ummar Jihar baki daya cewa, wannan sarauta da aka bawa dan uwanmu zai rike ta da muhimmacin gaske kuma ina da yakinin cewa zata kara dankon zumunci a tsakaninmu da Kanawa.”