✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Zazzau ya gargadi dillalan fili da gidaje

Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya gargadi dillalan fili da gidaje da su kiyayi sayar wa bakin da ba su sansu ba, don…

Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya gargadi dillalan fili da gidaje da su kiyayi sayar wa bakin da ba su sansu ba, don kauce wa sayar wa batagarin mutane da za su addabi jama’a.

Sarkin ya yi wannan gargadi ne a lokacin da al’ummar Masarautar Zazzau suka kai masa Gaisuwar Sallah a fadarsa da ke birnin Zariya.

Alhaji Shehu Idris wanda Iyan Zazzau Alhaji Bashari Aminu ya karanta jawabinsa ya ce rahotanni na nuna yadda ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke shigowa yankin Masarautar Zazzau suna sayen filaye da gidaje da kudaden da suke karba bayan sun yi garkuwa da mutane.

Sarkin ya umurci hakimai da dagatai da masu unguwanni da kuma ardo-ardo su sanya ido sosai a yankunansu domin ganin mutanen da ke shigowa yankunansu.

Game da yawaitar shaye-shaye da matasa ke yi, Alhaji Shehu Idris ya bayyana gamsuwa kan yadda ake samun ragowar lamarin a tsakanin matasa da sauran al’umma.

Ya bukaci iyaye su sanya ido tare da tsawatarwa domin kauce wa shiga cikin miyagun dabi’u.

Sarkin na Zazzau ya kuma shawarci manoma su himmatu wajen noma kada su karaya da ’yan bindiga da ke tsoratar da su saboda a samu isasshen amfanin gona.

Da ya juya kan mummunar dabi’ar nan ta lalata da kananan yara, ya bukaci jama’a su tona asirin mutanen da ke bata kananan yara domin su fuskanci hukunci.