✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarrafa Albarkatun Gona (2)

Na fara wannan makala ta ‘Sarrafa Albarkatun Gona’ a makon da ya gabata, inda  na kudiri aniyar fadakar da dan kasuwa a kan yadda zai…

Masara na daya daga cikin albarkatun gonar da za a iya sarrafawa domin kasuwannin gida da na wajeNa fara wannan makala ta ‘Sarrafa Albarkatun Gona’ a makon da ya gabata, inda  na kudiri aniyar fadakar da dan kasuwa a kan yadda zai iya sarrafa albarkatun gona da Allah Ya wadata mu da su a kasar nan domin sayarwa a garin da yake ko a manyan biranen kasar nan ko ya fidda su zuwa kasashen makwabtanmu ko kasashen ketare. A cikin makalar na sha alwashin zagaya shiyyoyin kasar nan shida domin yi wa dan kasuwa nunin irin albarkatun gona da Sarki Allah Ya albakace mu da su a cikin kowace shiryar, sannan kuma in dauke su daya bayan daya in yi bayanin yadda zai sarrafa kowannensu da kuma kasuwar da zai iya ci daga cikin kasuwannin da na lasafta.
  To idan mai karatu na biye da ni zai iya tunawa cewa a makon da ya gabata na lasafta irin wadannan albarkatun da ke shiyyar Arewa maso Yamma da ta kunshi jihohin Kano da Jigawa da Katsina da Zamfara da Sokoto da Kebbi da Kaduna. Na kuma duba albarkatun gona da ke shiyyar Arewa maso Gabas da ta kunshi jihohin Yobe da Borno da Taraba da Adamawa da Gombe da Bauchi. Na kuma yi bayanin yadda wadansu kasashe da ke da irin wadannan albarkatun wadanda ba su kai yawan namu ko ingancin namu ba amma su ke sarrafa su su fitar zuwa kasashen ketare su sayar su samu kudade masu yawan gaske. Na kum yi nunin cewa ‘yan kasuwar wadannan kasashe ne ke sarrafa irin wadannan albarkatu su fitar zuwa kasashen da za su sayar ba gwamnatocinsu ba. Kuma idan ma akwai wani tallafi da irin wadannan ‘yan kasuwa ke samu daga gwamnatocinsu to bai wuce irin wanda ‘yan kasuwar Najeriya ke samu daga gwamnatin tarayya ba idan sun yi irin wannan yunkurin. Kuma in dai ana biye da ni za a iya tuna wadansu makalu da na yi a bayani a kan ire-iren wadannan tallafin.
    To na samu wadansu wasiku daga masu karatu a kan wannan mukala, inda wasu suka yi mini nuni da wani kuskure da na yi a makalar ta baya, inda na yi misali da kasashen yankin ‘Norwegian’ da ke Turai a kan sarrafa madarar shanu suna sayar wa duniya suna samun kudin shiga, inda na lissafa kasashen da suka kunshi Norway da Holland da Denmark. To masu korafin sun ce na manta da Sweden, wacce in an hada da ita da wadansu kananan tsuburai za a kira yankin Scandinabia. A gafarce ni, kuskure ne. Wadansu kuma sun ce yayin da nake yin misalin irin albarkatun gona da ake samu a yankin Arewa maso Yamma na yi kuskuren rashin yin maganar masara da citta da doya da dankalin Turawa wadanda duk ake samunsu a Jihar Kaduna. Amma idan masu wannan korafi sun lura, ai misali na ke yi, ba wai na ce lallai sai na lissafa kowace albarkar gona da ake iya samu a kowace shiyya ba. Duk da haka dai na yi kuskure tunda wadannan abubuwa ne masu matukar mahimmanci da ake samu a shiyyar, musamman ma ganin yadda suka wadata a Jihar Kaduna, a yi mini afuwa.           
   Wani kuma korafin da na samu game da makalar ta baya shi ne cewa na yi bayanin kanana da manyan dabbobi da madararsu a matsayin albarkatun gona, cewa kuskure ne. To al’amarin ba haka yake ba. A duk lokacin da ake batun albarkatun gona, ana batun albarkatun noma da kiwo baki daya ne, saboda haka ba kuskure ba ne, idan ma akwai kuskure ya kasance ga rashin bayani da ban yi ba a farkon makalar cewa albarkatun gona sun hada abubuwan da noma da kiwo ke samarwa.
Zan tashi da bayanin albarkatun gonar da dan kasuwa zai iya samu ya sarrafa a shiyyar Arewa ta Tsakiyar Najeriya, idan Sarki Allah Ya kai mu mako na gaba.