✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarrafa Albarkatun Gona (3)

A zango na uku na wannan makala zan tashi da bayanin albarkatun gonar da dan kasuwa zai iya samu ya sarrafa a shiyyar Arewa ta…

A zango na uku na wannan makala zan tashi da bayanin albarkatun gonar da dan kasuwa zai iya samu ya sarrafa a shiyyar Arewa ta Tsakiyar Najeriya, kamar yadda na yi alkawari a makon da ya gabata. A makala ta farko da ta biyu na yi bayanai a kan iri-iren albarkatun gona da dan kasuwa zai iya samu daga shiyyoyin Arewa maso Yamma da Arewa maso gabas domin sarrafawa ya sayar a kasuwannin ciki da wajen kasar nan.
    Shiyyar Arewa ta Tsakiya ta kunshi jihohin Binuwai da Filato da Kwara da Nasarawa da Neja da Kogi da yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja. Albarkatun gona da aka fi samu domin sarrafawa a wannan shiyyar sun hada da doya da rogo da acca da dankalin Turawa da karas da kukumba waken salad iri-iri da koren tattasai da kwakwar man ja da shinkafa da da kifi da kayan marmari, musamman ma lemo da ayaba.
 Sai kuma shiyyar Kudu maso Yamma, wacce ta kunshi jihohin Legas da Oyo da Ekiti da Ogun da Ondo da Oshun. Akwai albarkatun gona masu yawa da dan kasuwa zai iya sarrafawa domin kasuwanninmu na gida da na waje, kamar rogo da agada da agusi da kifi da goro da koko da kayan marmari irin su kwakwa da lemo da abarba da ayaba da agwaluma da mangwaro.
   Shiyyar Kudu maso Gabas ta kunshi jihohin Abiya da Anambara da Inugu da Imo da Ebonyi. Albarkatun gona da aka fi samu domin sarrafawa daga wannan shiyya sun hada da kwakwar manja da kwakwa da rogo.
Ita kuma shiyyar Kudu maso kudu ta hada da jihohin Ribas da Kuros Ribas da Akwa Ibom da Bayelsa da Edo da Delta. A wannan shiyyar akwai arbarkatun gona da za a iya sarrafawa irin su rogo da kwakwar manja da agada da kifi da kwakwa da abarba da sauran su.
Idan mai karatu na biye da ni, na yi bayanin daukar irin wadannan albakatu domin fadakar da dan kasuwa irin bukatar da ake da ita a kasuwannin gida Najeriya da kasuwannin kasashen waje, walau kasuwannin kasashen da ke makwabtaka da mu, ko kuma ma na kasashen ketare. Na kuma ce zan yi bayanin siffar yadda masu bukatar irin wadannan albarkatu ke bukatarsu da kuma ka’idojin da masu saye ke bukatar samunsu. Zan kuma ba dan kasuwa shawarwari a kan inda zai samu wadannan albarkatun gona da yadda zai sarrafa su domin karbuwarsu a wadannan kasuwanni.
    Na yi makalu a baya a kan fitar da kayayyaki zuwa kasashen duniya, kama daga kasashen Yammacin Afrika da ke makwabtaka da mu, ya zuwa kasashen ketare. Amma duk da haka zan maimaita wadannan hanyoyi da ka’idojin fitar da wadannan kayayyaki, musamman ma yadda wadannan ka’idoji suka shafi kowace hajar da za a fitar. Zan kuma kuma bayar da hasken wuraren da ake bukatar kowace haja a cikin gida Najeriya ko kuma kasashen da ake bukatarta a duniya. Sannan kuma in  duba tallafin da dan kasuwa zai iya samu dangane da irin abin da zai fitar ya zuwa kasashen duniya.
 Zan fara daukar wadannan albarkatun gona da dai-dai da dai-dai in yi wadannan bayanai a kansu idan Allah Ya kai mu makon gobe.