✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarrafa Albarkatun Gona: karo (2)

A makon da ya gabata na yi shimfida a kan karo, inda na yi bayanin yadda yake da amfaninsa a gargajiyence da kuma abubuwan amfani…

A makon da ya gabata na yi shimfida a kan karo, inda na yi bayanin yadda yake da amfaninsa a gargajiyence da kuma abubuwan amfani da masana’antu ke samarwa daga sarrafa shi. Na kuma yi bayanin jihohin da ake samunsa, da kuma mahimmancin Najeriya a kasuwar karo ta duniya, inda take da matsayi na biyu bayan kasar Sudan. Makalar ta kuma yi bayanin yawan karon da ake samu a duniya da kuma kason da Najeriya ke samarwa a kasuwar karo ta duniya. Sannan na yi bayanin kasashen da ke sayen karo a duniya, musamman ma wadanda ke sayen karon daga Najeriya.
Haka kuma idan mai karatu bai shafa’a ba, a makon da ya gabata din ne na yi bayanin irin launukan karo kashi uku da ake samu daga Najeriya, da kuma mahimmancin su ga masana’antu da ke sayen su a kasashen ketare, saboda haka wannan launi da mahimmancin kowane  karo ke bambanta darajar farashinsa a nan gida da kasuwannin ketare. Hakan ya sa dole dan kasuwa ya mayar da sanin bambancin launin karo ya kasance masa darasin farko a cikin wannan harka.
Wani abu da nake so in fadakar da dan kasuwa mai sha’awar wannan harka, shi ne sabanin dukkanin albarkatun gona da na yi bayaninsu a baya, karo na matukar karanci a kasuwannin duniya, saboda haka bukatarsa ga masana’antu masu sarrafa shi kullum habaka take yi, saboda haka akwai alheri kwarai cikin harkarsa. Bugu da kari kuma, akwai yunkuri daga kamfanonin da ke sarrafa shi a manyan kasashen duniya, musamman ma Amurka, da manyan kungiyoyin duniya masu zaman kansu da hukumomin kasa-da- kasa da gwamnatoci da ke kokarin habaka nomansa da kasuwancinsa. Na yi tsokaci a makalar farko a kan irin wannan yunkuri, inda na yi bayanin yadda gwamnatin tarayyar Najeriya ta fito da tsarin noma da kasuwancin karo domin inganta hanyoyinta na samun kudin shiga da ba ta hanyar fitar da gurbataccen mai ba, da ake ce wa ‘Nigeria Gum Arabic Sector Debelopment Program’.
Na yi bayanin makasudin wannan tsarin da ake cewa an yi shi ne domin taimaka wa  manoman karo da masu sarrafa karo da masu fitar da karo zuwa kasashen waje ne, domin su inganta yawa da martabar karo girediwan domin sayar da shi a kasuwannin Amurka. Domin tabbatar da haka na ce akwai wani kamfani mai suna ‘ARD Inc’ na Amurka da ke aiki da manoma da masu fitar da karo zuwa kasashen waje a duk sassan kasar nan da ake samun karo, domin samun biyan wannan bukatar.   
Wannan yunkuri ba a nan ya tsaya ba, irin wadannan kungiyoyi da hukumomi da gwamnatoci na kokarin bunkasa noman karo a Najeriya da sauran kasashen da ake samar da shi, domin hana kwararowar hamada; domin wadannan kasashe suna iyaka da Hamada, kamar kasar Sudan, ko kuma sun a iyaka da kasashen da hamada ta mamaye, kamar yadda Najeriya ke da iyaka da kasar Nijar wacce Hamada ta mamaye.  Idan mai karatu kuma zai lura, jihohin da na yi bayanin ake samun karo, na da iyaka da kasar ta Nijar, kamar su Yobe da Barno da Jigawa da Adamawa da  Zamfara da Katsina da Kebbi da Taraba da Sakkwato. Wannan yunkuri zai ba dan kasuwa hasken ingancin da kasuwar karo ke da shi a duniya, hakan kuma zai kasance manuniyar alherin da ke cikin harkar ta karo.
Farashin tan din karo a kasuwannin duniya na kamawa daga Dalar Amurka 575 (kimanin Naira dubu 96) zuwa 995 (kimanin Naira dubu 155), wanda ya danganta da martabar karon. Farashin tan din karo a Najeriya na kamawa daga Naira dubu 35 zuwa Naira dubu 50, shi ma ya danganta da ingancin karon.